Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Yaba Wa Sojoji Kan Murƙushe ’Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force (North West) Operation Fansan Ya...

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force (North West) Operation Fansan Yamma bisa manyan nasarorin da suka samu a yaƙi da ’yan bindiga a sassan jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar 10 ga watan Mayun 2026, ya bayyana cewa dakarun rundunar sun kai wani gagarumin farmaki mai cike da tsari da haɗin kai a safiyar ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, 2026, a ƙananan hukumomin Kaura Namoda da Birnin Magaji na jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce, bayan artabun da aka yi da miyagun, jami’an tsaron sun kashe shugabannin ƙungiyoyin ‘yan bindiga uku tare da ƙwato tarin makamai da harsasai. Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, bindigar mashin gon guda ɗaya, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, gidan harsashin bindiga guda bakwai da kuma harsasai 571.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana sabon farmakin da rundunar sojin ta ƙaddamar a matsayin abin yabawa kuma da ya zo a kan lokaci, musamman sakamakon nasarar da aka samu a ranar 10 ga watan Mayun 2026, inda aka tarwatsa wani babban taron shugabannin ‘yan ta’adda tare da kashe wasu manyan kwamandojinsu.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ‘yan ta’addar sun taru a wani buyayyen wuri da ke ƙauyen Tumfa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi, domin tsara sabbin hare-hare da ayyukan ta’addanci kan al’ummomin jihar.

Bangaren rundunar sojin sama ya kai wani ingantaccen harin sama kan maboyar ‘yan ta’addar, inda aka lalata ginin da suke amfani da shi a matsayin wurin taronsu.

Gwamna Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar Zamfara na ci gaba da bai wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro cikakken goyon baya da kayan aiki domin yaƙi da matsalar tsaro a jihar.Gwamna Lawal Ya Yaba Wa Dakarun Soji Kan Nasarorin Da Suka Samu Kan ’Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force (North West) Operation Fansan Yamma bisa manyan nasarorin da suka samu a yaƙi da ’yan bindiga a sassan jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar 10 ga watan Mayun 2026, ya bayyana cewa dakarun rundunar sun kai wani gagarumin farmaki mai cike da tsari da haɗin kai a safiyar ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, 2026, a ƙananan hukumomin Kaura Namoda da Birnin Magaji na jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce, bayan artabun da aka yi da miyagun, jami’an tsaron sun kashe shugabannin ƙungiyoyin ‘yan bindiga uku tare da ƙwato tarin makamai da harsasai. Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, bindigar mashin gon guda ɗaya, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, gidan harsashin bindiga guda bakwai da kuma harsasai 571.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana sabon farmakin da rundunar sojin ta ƙaddamar a matsayin abin yabawa kuma da ya zo a kan lokaci, musamman sakamakon nasarar da aka samu a ranar 10 ga watan Mayun 2026, inda aka tarwatsa wani babban taron shugabannin ‘yan ta’adda tare da kashe wasu manyan kwamandojinsu.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ‘yan ta’addar sun taru a wani buyayyen wuri da ke ƙauyen Tumfa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi, domin tsara sabbin hare-hare da ayyukan ta’addanci kan al’ummomin jihar.

Bangaren rundunar sojin sama ya kai wani ingantaccen harin sama kan maboyar ‘yan ta’addar, inda aka lalata ginin da suke amfani da shi a matsayin wurin taronsu.

Gwamna Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar Zamfara na ci gaba da bai wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro cikakken goyon baya da kayan aiki domin yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

No comments