Daga Ibrahim Muhammad Jam’iyyar APC ta tabbatar da Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar kujerar majalisar ...
Daga Ibrahim Muhammad
Jam’iyyar APC ta tabbatar da Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar kujerar majalisar jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gezawa a zaɓen 2027.
Wakilan jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Ahmad Haruna Bichi, tare da wakilan uwar jam’iyyar APC ta jihar Kano, jami’an hukumar zaɓe ta ƙasa, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron tabbatar da takarar, wanda ya gudana ranar Laraba a sakatariyar APC ta ƙaramar hukumar Gezawa.
Da yake jawabi bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takara, Hon. Tsamiyar Kara ya gode wa Allah bisa nasarar da aka samu da kuma haɗin kan da aka nuna yayin taron.
Ya bayyana ranar a matsayin ranar farin ciki da nuna goyon baya daga al’ummar Gezawa da magoya bayan jam’iyyar APC.
Haka zalika, ya gode wa al’ummar ƙaramar hukumar Gezawa bisa ƙauna da goyon bayan da suke ba shi, tare da yaba wa jagoran APC na Gezawa, Murtala Zainawa, da sauran shugabannin jam’iyyar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar sa.
Ya kuma yaba wa uwar jam’iyyar APC ta jihar Kano bisa jagorancin da ta bayar, wanda ya sa aka gudanar da zaɓen fidda gwani cikin lumana da kwanciyar hankali a faɗin jihar.
Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara ya kuma yaba wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa abin da ya kira dattako, jagoranci nagari da son zaman lafiya, yana mai cewa hakan ne ya taimaka wajen gudanar da zaɓen fidda gwani cikin adalci da gaskiya.
Ya yi addu’ar Allah Ya tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a kan mulkin jihar Kano tare da ba shi wa’adi na biyu, sannan Ya ba su nasarar sake lashe kujerar majalisar jiha ta Gezawa.
Tsamiyar Kara ya ce ya gudanar da siyasar sa cikin biyayya ga jam’iyyar APC ba tare da cin mutuncin kowa ko amfani da kalaman ɓatanci ba.
Ya kuma yi kira ga sauran waɗanda suka fafata da shi wajen neman tikitin takarar da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
A cewarsa, babu abin da ya fi muhimmanci a gare su kamar ganin APC ta samu nasara, yana mai jaddada cewa za su ci gaba da biyayya ga jam’iyyar da shugabanninta tare da gyara duk wani gibi domin cimma nasara.
Hon. Tsamiyar Kara ya tabbatar da cewa zai yi aiki tuƙuru domin ganin APC ta samu nasara a matakin ƙaramar hukumar Gezawa, jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
No comments