Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Mutane 6,842 Sun Ci Gajiyar Magani Kyauta Na Gwamnatin Jihar Zamfara Kashi Na 17

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa, ta gudanar da aikin kula da marasa lafiya 6,842 ta hanyar babban shirin tallafin lafiya...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa, ta gudanar da aikin kula da marasa lafiya 6,842 ta hanyar babban shirin tallafin lafiya kyauta da aka tanada domin yi wa al’umma tiyata da sauran kulawar lafiya ba tare da biyan kuÉ—i ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an ce an fara aiwatar da shirin tun daga watan Agustan shekarar 2023 a manyan cibiyoyin lafiya da suka haɗa da Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, Babban Asibitin Gusau, Cibiyar Kula da Ido ta Gusau da kuma Asibitin Farida.
Sanarwar ta ce, kashi na 015, 016 da 017 na shirin tallafin lafiyar an gudanar da su daga ranar Juma’a 1 ga watan Mayu zuwa Lahadi 17 ga watan Mayun 2026.

A cewar gwamnatin jihar, shirin ya haÉ—a da yi wa marasa lafiya tiyatar ciwon ido na yanar ido, wato cataract, cututtukan kumburin mara irin su hernia da hydrocele, gyaran matsalar yoyon fitsari ga mata (VVF), tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa, shirin na daga cikin manufofin Gwamna Dauda Lawal na magance manyan matsalolin lafiya da ake fama da su domin inganta rayuwa da walwalar al’ummar jihar Zamfara.

“Shirin Tallafin Lafiya na Musamman da aka gyara yana ba da damar samun kulawar lafiya kyauta ga masu fama da cututtukan da suka haÉ—a da cataract, hernia, hydrocele da kuma gyaran matsalar yoyon fitsari ga mata,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa baya ga bayar da magani, ana amfani da shirin wajen ilmantar da jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da tsaftar rayuwa.

An bayyana cewa an gudanar da ayyukan jinyar ta hanyar amfani da tsarin tantance marasa lafiya ta fasahar sadarwa domin kai kulawar ƙwararru zuwa yankunan karkara da ƙananan birane a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Sanarwar ta ce, kashi 17 da aka gudanar zuwa yanzu sun haÉ—a da tiyata 5,282 da kuma jinyar wasu marasa lafiya 1,200, inda aka kula da masu cututtukan kumburi da masu fama da cataract, mata masu matsalar VVF da sauran nau’o’in tiyata na musamman da na gama gari.

Gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da irin wannan tallafin lafiya musamman domin taimaka wa marasa ƙarfi da masu buƙata a faɗin jihar.

No comments