Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi lambar yabo ta ƙwarewa daga Hukumar Daidaita Shirye-shiryen Tallafin Jinƙai ta Ƙasa...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi lambar yabo ta ƙwarewa daga Hukumar Daidaita Shirye-shiryen Tallafin Jinƙai ta Ƙasa (NASSCO) bisa irin ƙoƙarin gwamnatin sa wajen tabbatar da mulki na adalci da kuma aiwatar da shirye-shiryen kare marasa ƙarfi a jihar Zamfara.
An bai wa gwamnan lambar yabon ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin ƙananan hukumomi da hukumar ta shirya a ɗakin taro na Transcorp Congress Hall da ke Abuja.
Hukumar NASSCO wata hukuma ce ta tarayya ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, wadda ke aiwatar da shirye-shiryen tallafawa marasa galihu da ƙarfafa rayuwar masu rauni a faɗin ƙasar nan.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya da sauran abokan hulɗar ci gaba bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen ƙarfafa tsarin kariyar zamantakewa a Nijeriya.
Ya ce faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa tare da haɗa Lambar Shaidar Ɗan ppl plß Ƙasa (NIN) a cikin tsarin ya taimaka wajen inganta gaskiya da riƙon amana wajen rabon tallafi.
A cewarsa, wannan taro ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar ƙarfafa tsarin kariyar jama’a, musamman a jihohin da ke fama da matsalolin tsaro kamar Zamfara.
“Yanzu kariyar zamantakewa ta wuce batun tallafi kawai, ta zama wata muhimmiyar hanya ta tabbatar da tsaro, rage talauci da gina juriya a tsakanin al’umma,” in ji gwamnan.
Ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a Zamfara ta haddasa raba mutane da matsugunansu, durƙushewar hanyoyin samun abinci da kuɗaɗen shiga, lamarin da ya fi shafar mata, yara, nakasassu da mazauna karkara.
Gwamnan ya jaddada cewa dole ne shirye-shiryen tallafi su kasance masu tsari, gaskiya da amfani da sahihan bayanai domin tabbatar da cewa tallafin ya isa hannun waɗanda suka fi buƙata.
Ya kuma nuna muhimmancin ƙananan hukumomi wajen hulɗa da al’umma, tantance bayanai, tallafa wa tsarin shaidar mutum da kuma sanya ido kan yadda ake aiwatar da shirye-shiryen tallafi.
Gwamna Lawal ya ƙara da cewa, haɗa lambar NIN da Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa zai taimaka wajen rage maimaita bayanai, ƙarfafa gaskiya da kuma inganta yadda ake aiwatar da shirye-shiryen tallafi.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa fasaha kaɗai ba za ta warware matsaloli ba idan ba tare da kyakkyawan shugabanci, riƙon amana da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki ba.
Gwamnan ya ce, gwamnatin Zamfara na goyon bayan duk wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, tare da haɗa kai da hukumomi da ƙungiyoyin ci gaba masu ruwa da tsaki a harkar kare rayuwar al’umma.
Ya kuma bayyana cewa ci gaba mai amfani ya kamata ya zarce rabon kuɗaɗe kawai, ya haɗa da bunƙasa sana’o’i, horas da matasa, noma, lafiya, ilimi, shigar jama’a cikin harkokin kuɗi da kuma ƙarfafa juriya a tsakanin al’umma.
Da take miƙa lambar yabon ga gwamnan, Babbar Mai Kula da Hukumar NASSCO ta Ƙasa, Dakta Funmi Olotu, ta ce an ba shi wannan karramawa ne saboda irin jajircewar gwamnatinsa wajen inganta kariyar zamantakewa da tabbatar da shugabanci na adalci a Zamfara.
No comments