Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wasu Dokokin Zartarwa da za su kafa sabon tsarin gudanar da harkokin ilim...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wasu Dokokin Zartarwa da za su kafa sabon tsarin gudanar da harkokin ilimi a jihar, tare da ƙaddamar da rabon Manhajar Karatu ta Ƙasa ga makarantun gwamnati.
Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ne a ranar Talata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa dokokin zartarwar sun ƙunshi sabbin tsare-tsaren gudanar da harkokin kuɗaɗen ilimi, kare makarantu, tantance nau’o’in makarantu, tabbatar da ingancin ilimi, kula da lafiyar ɗalibai da kuma inganta tsaro a makarantu.
Sanarwar ta ce, gyare-gyaren sun kuma shafi yadda za a gudanar da makarantu, tsarin ciyar da ɗalibai, walwalar ɗalibai, tabbatar da tsaron zirga-zirgar makaranta, aiwatar da shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe Schools Initiative) da kuma tsara yadda ake gudanar da bukukuwan kammala karatu.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta kuma gabatar da sauye-sauye da suka haɗa da gudanar da jarrabawa a tsari guda, inganta ayyukan kula da lafiyar makarantu, naɗin shugabannin makarantu bisa cancanta, bunƙasa ilimin bai ɗaya, da kuma ƙarfafa koyar da Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), Ilimin Fasaha da Sana’o’i (TVET) da ilimin zamani na fasahar dijital.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ilimi ya fi kasancewa kawai wata hidimar zamantakewa.
Ya ce ilimi shi ne mafi ƙarfi wajen rage talauci, samar da zaman lafiya, ƙarfafa tsaro, haɓaka tattalin arziki da kuma shirya matasa domin fuskantar ƙalubalen duniya mai dogaro da ilimi.
“A yau muna mayar da wannan ƙuduri zuwa matakan da za su ɗore ta hanyar sanya hannu da kuma ƙaddamar da waɗannan Dokokin Zartarwa.
“Waɗannan dokoki ba umarni ne daban-daban ba. Tsarin mulki ne cikakke da aka tsara domin inganta tafiyar da makarantu, ƙarfafa riƙon amana, kare kadarorin ilimi na gwamnati, inganta yadda ake samar da kuɗaɗen ilimi, tabbatar da tsaro, ɗaga darajar ilimi, inganta sakamakon karatu da kuma shirya yaranmu domin ƙarni na 21,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa, tsawon shekaru an fi mayar da hankali wajen gina azuzuwa da dakunan gwaje-gwaje, amma ƙwarewa ta nuna cewa gine-gine kaɗai ba su wadatar wajen samar da ingantaccen ilimi.
Tun da farko, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Zamfara, Abdulmalik Abubakar Gajam, ya ce nasarar kowace manhajar gyaran ilimi na dogara ne da haɗin gwiwar gwamnati, malamai, iyaye, al’umma, sarakunan gargajiya, abokan hulɗar ci gaba da kuma masu zaman kansu.
Ya bayyana cewa manufar waɗannan gyare-gyare ita ce tabbatar da makarantu masu tsaro, ingantaccen shugabanci, lafiyar ɗalibai, kyakkyawan koyarwa, sakamako mai inganci a fannin ilimi da kuma ƙara yawan amincewar jama'a da tsarin ilimin jihar.
No comments