Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ƙungiyar Mabiya Ahlulbaiti Ta Sake Jaddada Muhimmancin Zaman Lafiya da Ingantacciyar Gwamnati a Kano

Daga Muhammad Saƙafa  Ƙungiyar Mabiya da Masoya Ahlulbaiti da ake kira 'Ahlulbaiti Political Organization' sake jaddada ...

Daga Muhammad Saƙafa 

Ƙungiyar Mabiya da Masoya Ahlulbaiti da ake kira 'Ahlulbaiti Political Organization' sake jaddada aniyarta na tabbatar da zaman lafiya, ingantacciyar gwamnati, daidaito da gaskiya a jihar Kano, tare da yin kira ga al’ummar jihar da su haɗa kai wajen gina al’umma mai ɗorewa.

A cikin wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun shugabanta na jihar Kano, Alhaji Adamu Kabiru Auduwa, ƙungiyar ta ce bambancin da ke tsakanin al’umma bai kamata ya zama dalilin rarrabuwa ba, sai dai ya zama wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ci gaban Kano da Nijeriya baki ɗaya ya dogara ne kan samar da kyakkyawar mu’amala tsakanin ƙabilu, addinai da masu bambancin ra’ayoyin siyasa. 

Ta kuma yi kira ga shugabanni da ’yan ƙasa da su fifita muradun jama’a a kan son kai, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen siyasa da tattalin arziƙi.

Ahlulbaiti ta kuma yi kira ga ’yan siyasa da su gudanar da bisa manufofi kyawawa, tare da guje wa kalaman ɓatanci da ƙiyayya da duk wani abu da ka iya haifar da rikici a tsakanin al'umma.

Ta sanar da shirin ƙaddamar da tattaunawa tsakanin al’umma mai taken “Mu sa Kano a gaba don zaman lafiya” a ƙananan hukumomi 44 na jihar, domin ƙarfafa fahimtar juna da hana rikici tun kafin ya faru.

Dangane da ingantacciyar gwamnati kuwa, ƙungiyar ta ce shugabanci nagari ya kamata ya kasance mai gaskiya, mai buɗaɗɗiyar zuciya, kuma mai sauraron buƙatun jama’a. 

Ta buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa da samar da yanayi mai kyau ga ’yan kasuwa da masu sana’o’i.

Haka kuma, ƙungiyar ta jaddada muhimmancin daidaito da shigar kowa cikin harkokin mulki, musamman mata, matasa da masu buƙatu na musamman. 

Ta ce daidaito ba kyauta ba ne, haƙƙi ne, tare da bayyana cewa za ta faɗaɗa shirye-shiryen kula da “Mata da shugabanci na gari” da shigo da matasa a cikin jagoranci domin ƙarfafa shigar jama’a cikin harkokin mulki.

A ƙarshe, Ahlulbaiti Political Organization ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano, jam’iyyun siyasa, sarakuna, shugabannin addinai, kafafen yaɗa labarai da sauran ’yan ƙasa da su haɗa kai wajen gina Kano mai zaman lafiya, adalci da kyakkyawar gwamnati, tana mai cewa: “Mu zaɓi tattaunawa maimakon rarrabuwa, hidimta wa jama'a maimakon son kai, da haɗin kai maimakon rikici.”

No comments