Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamnatin Zamfara Za Ta Bai Wa Mutane 36,176 Hannun Jari A Kamfanin Ɗangote

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da wani shiri na bai wa mazauna jihar 36,176 hannun jari a rukunin kamfanonin Dangote, a wani ...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da wani shiri na bai wa mazauna jihar 36,176 hannun jari a rukunin kamfanonin Dangote, a wani yunƙuri na faɗaɗa damar zuba jari ga jama’a da kuma ƙarfafa musu tattalin arziki.

Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai da Agajin Gaggawa ta jihar ce ta bayyana cewa shirin zai bai wa mazauna damar cin gajiyar damarmakin zuba jari da kuma shiga cikin harkokin kasuwanci a ƙasar.

A ƙarƙashin shirin, ana sa ran kowane mai cin gajiyar tallafin zai samu kusan hannun jari 20 ta hanyar sayar da hannun jarin Ɗangote ga jama’a a karon farko (Initial Public Offering — IPO).

Za a gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Ma’aikatun Harkokin Jin Ƙai da Agajin Gaggawa da Kuɗi na jihar, da kuma Kamfanin Zuba Jari na Zamfara.

Za a gudanar da aikin ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Jin Ƙai da Agajin Gaggawa na jihar, Salisu Musa Tsafe Kainuwa.

A cewar ma’aikatar, za a zaɓi waɗanda za su amfana daga ƙananan hukumomi 14 na jihar. Za a ware mutum 2,261 ga kowace ƙaramar hukuma daga cikin 13, yayin da Gusau, babban birnin jihar, za ta samu mutum 4,522.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa shirin zai ƙunshi masu buƙata ta musamman, ciki har da masu nakasa, domin tabbatar da cewa an bai wa kowane ɓangare na al’umma damar cin gajiyarsa.

Ta ƙara da cewa Gwamna Dauda Lawal ne ya amince da shirin domin faɗaɗa damar mazauna jihar ta fuskar zuba jari da kuma taimaka musu su samu ’yancin kai na kuɗi.

Gwamnatin jihar ta ce shirin na daga cikin manyan manufofinta na agajin jinƙai da bunƙasa tattalin arzikin jama’a. Ta kuma bayyana cewa nan gaba za ta sanar da wasu shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki da za su fi mayar da hankali kan mata da matasa.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a iya tantance sahihancin bayanan ma’aikatar game da yawan hannun jarin da za a bai wa kowane mutum, ribar da ake sa ran za a samu, da kuma biyan kuɗin da ake buƙata domin sayen hannun jarin ba.

Sanarwar ba ta fayyace farashin kowane hannun jari, jimillar kuɗin da za a zuba a shirin, ko kuma tsarin da za a bi wajen raba hannun jarin ga waɗanda suka cancanta ba.

No comments