Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

NDC Ta Miƙa Ƙorafinta Ga INEC Kan Rashin Sanya Sunan Gwarzo

Daga Hadi Bawa  Jam’iyyar NDC a jihar Kano ta ce ta miƙa takardar ƙorafi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin a...

Daga Hadi Bawa 

Jam’iyyar NDC a jihar Kano ta ce ta miƙa takardar ƙorafi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin a dawo da sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓen gwamna na shekarar 2027.

TNL HAUSA ta samu rahoton cewa, Hon. Hamza Ahmad Telan Mata ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta musamman da ya wallafa, inda ya ce jam’iyyar NDC ta cika dukkan sharuɗɗan da ta gindaya, tare da buƙatun da INEC ta tanada.

Ya bayyana cewa, bisa ga cikar waɗannan sharuɗɗa, jam’iyyar ba ta ga dalilin da zai sa a bar sunan ɗan takararta a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar Kano ba.

A cewarsa, INEC ta karɓi takardar da aka miƙa mata, kuma jam’iyyar na fatan Hukumar za ta duba ƙorafin, tare da gyara abin da ta bayyana a matsayin kuskure, domin dawo da sunan Gwarzo cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna na zaɓen 2027.

Hon. Telan Mata ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar NDC da na Kwankwasiyya da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da addu’a da jajircewa yayin da suke jiran matakin da Hukumar za ta ɗauka.

Kamar yadda TNL HAUSA ta ruwaito, sunayen wasu 'yan takarar gwamna uku daga jam'iyyar PDP da NDC ba su fito ba a cikin jerin sunayen da INEC ta fitar.

No comments