Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta'aziyyar Kwamishinan Kasuwanci, Tasiu Shinkafi

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna alhinin sa na rasuwa Kwamishinan harkar kasuwanci na jihar, Tasiu Musa Shinkafi. Allah...

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna alhinin sa na rasuwa Kwamishinan harkar kasuwanci na jihar, Tasiu Musa Shinkafi.

Allah ya yi wa Shinkafi rasuwa ne a Larabar nan da ta gaba a wani asibiti da ke Kaduna sakamakon gajeruwar rashin lafiya, yana da kimanin shekaru 50.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, Gwamna Lawal ya bayyana wannan rasuwa a matsayin babban rashi ga gwamnati da al'ummar jihar Zamfara.

Gwamnan ya ce, "Bisa imani da miƙa al'amura ga Allah Maɗaukaki, muka samu labarin rasuwar Kwamishinan Harkar Kasuwanci, Tasiu Musa Shinkafi.

Rasuwar Tasiu, ba wai rashi ne ga iyalai, 'yan uwa da gwamnati kaÉ—ai ba, rashi ne ga É—aukacin al'ummar Zamfara.

"Za a rinƙa tuna Tasiu da jajircewa, gaskiya da aiki tuƙuru ga jihar Zamfara.

"Ya yi kyakkyawan aiki a lokacin da ya ke Kwamishinan harkar matasa da wasanni, kafin daga bisani aka dawo da shi ma'aikatar kasuwanci.

"A matsayin sa na muhimmin ma'aikaci a gwamnati na, sannan ɗan uwa na a aiki, a kullum za mu rinƙa tuna gudumawar sa a harkokin gwamnati, siyasa da yi wa jama'a hidima."

A ƙarshe Gwamna Lawal ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa kurakuran sa, ya ba iyalan sa haƙurin jure wannan rashi.

No comments