Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Mun Shiyar Karba Mulki A 2027 Jam’iyyar Labour

Daga Abubakar Rabilu Gombe Jam’iyyar adawa ta Labour Party ta bayyana cewa suna shirin karbar mulki a wasu jihohi da ma Najeriya...


Daga Abubakar Rabilu Gombe

Jam’iyyar adawa ta Labour Party ta bayyana cewa suna shirin karbar mulki a wasu jihohi da ma Najeriya a zaben shekara ta 2027 muddin mutane suka gamsu da kyawawan manufofin su.

Shugabar Mata ta kasa ta jam’iyyar Dudu Poloma Manuga,ita ce

Ta bayyana hakan a wani taro da jam’iyyar ta kira ‘ya’yan ta da shugabani da ya gudana a Gombe.

Dudu Manuga, ta kira shugabanin jam’iyyar da cewa su ci gaba da snana’ar da jama’a irin kyawawan manufofin jam’iyyar ta su da kuma irin tsare-tsaren da suke yi domin kawo wa kasar nan ci gaba ida suka karbi mulki saboda gazawar jam’iyyar da ke mulki a halin yanzu
A nasa jawabi shugaban jam’iyyar na jihar Gombe Ambasada Benjamin Abner Mamman, cewa yayi jam’iyyar tana aiki ba dare ba rana wajen ganin ta hada kan ‘ya’yan ta saboda su jajirce wajen ganin idan lokaci yayi sun yiwa jam’iyyar aiki tukuru domin samun nasara ganin cewa kasar na tangal-tangal ta gaza seti.

Benjamin Abner, ya bada tabbacin cewa jam'iar za ta samar da kyakyawan shugabanci wajen samar da ci gaba mai ma'ana ga al'umma muddin aka zabe ta

A jawaban su daban-daban wasu Dattawan jam'iyar ta Labour a jihar Umar Action, da Bala Jibrin, jinjinawa kokarin shugabannin nasu suka yi bisa aiwatar da tsare-tsare da manufofin jam'iyar.

Da yake tsokaci a madadin shugabannin jam'iyar na kananan hukumomi goma sha daya na jihar Gombe,  shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Yamaltu Deba, Babayo Muhammad, ya bukaci dukkan 'ya’yan jam'iyyar ne da su hada kai kuma su rika girmama shugabannin su domin idan ana tafiya ba tsari ba yadda za’ayi a samu nasarar da ake bukata

Taron dai na fara tauna tsakuwa ne a shirye-shiryen su na motsa jam’iyyar ganin cewa nan gaba kadan za’a fara hada-hadar siyasa dan fuskantar zabukan shugabanin jam’iyyar daga matakin kasa zuwa jiha sannan a fita filin daga dan babban zabe na gamagari.

No comments