Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Shugaban NYSC yayi kira ga Shugabannin kananan Hukumomi su inganta rayuwar al'umma.

Daga Zubairu M. Lawal   Shugaban Hukumar kula 'Yan-yima kasa hidima ya roki kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa AL...


Daga Zubairu M. Lawal 


 Shugaban Hukumar kula 'Yan-yima kasa hidima ya roki kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa ALGON databa  da fifiko sosai wajen inganta tsaro, walwala da jindadin 'ga al'umman kasa da yan-yima kasa hidima da ake Turasu zuwa yankunansu.

   Darakta Janaral na Hukumar Birgediya Janaral Yusha'u Ahmed shine yayi rokon a wajen taron majalisar zastarwa na  kungiyar ALGON ta qasa .

daya gudana ranar Juma'a 19/7/2024  a lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Yace; ya ziyarci wannan taron na ALGON na jihohi 36 da yake gudana a Nasarawa domin taya Shugabannin kananan Hukumomi murnar samun yancin cin gashin kai da Babban kotun kasa ta tabbatar masu.

A dalilin haka yake kira ga Shugabannin kananan Hukumomi dasu karkatar da akalarsu wajen kulawa da matasa yan yima kasa hidima da ake turawa garuruwansu.

Yace; hakan zai baiwa masuyi kasa hidima damar gudanar da ayyukan da ya kaisu cikin nasara.


Birgediya Janaral Yusha'u Ahmed yace; akwai wasu Shugabannin kananan Hukumomi da suke taimakama yan yima qasa hidima da guraren kwana harma da tallafin yau da kullun.amma wasu guraren ba kamar hakaba.

Yace; anfi tura yan yima kasa hidima yan kunan kananan Hukumomi a duk lokacin.

Yace; yan yima kasa hidima sun sadaukarwa wajen bada fifiko kan ilumi da kiwon lafiya da tsaftar muhalli da sauransu.

Shima a nasa jawabin mai masaukin baki Shugaban kungiyar Shugabannin ALGON kuma Shugaban karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Ma'azu Maifata.

Ya godewa Darakta na Kungiyar yiwa kasa hidima saboda tunasar dasu mahimman wasu ayyukan da ya rataya a wuyarsu.

Mai fata yace; a taron majalisan zartarwan Kungiyar karo na 48, zasu tatauna abubuwa da suka shafi maida hankali wajen abubuwan da suka addabi al'umma. Kamar lamarin tsaro da kiwon lafiya yadda za a kula da Samar da kananan Asibitochin sha katafi, da gyaran tituna da magudanan ruwa da tsaftar muhali da sauransu.

No comments