Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah ya yabawa Bola Ahmad Tinubu saboda kirkiro Ma'aikatan kiwo a Najeriya

Daga Zubairu M. Lawal Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah Kautal hore ta qasa Alhaji Bello Badejo ya jinjinawa Shugaban ka...


Daga Zubairu M. Lawal

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah Kautal hore ta qasa Alhaji Bello Badejo ya jinjinawa Shugaban kasar Najeriya Alhaji Bola Ahmad Tinubu saboda kirkiro Ma'aikatan kiwo a tsarin Najeriya.

Da yake zanatawa da manema labarai a ofishinsa dake Maliya a karamar hukumar Karu cikin jihar Nasarawa.

Shugaban yace; tun a Gwamnatin marigayi Alhaji Umar Musa Yar'adu suketa fadi tashi domin ganin an kirkiro wannan Ma'aikatan amma har yar'adu ya koma ga Allah lamarin bai yuhu ba.

Lokacin mulkin Jonathan shima sun shiga sun fita. Badejo yace sunyi fama a Gwamnatin Muhammad Buhari amma shima bai kirkiro wannan Ma'aikatan ba.

Yace; dole mu godewa Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu saboda kirkiro wannan Ma'aikatan.

Bello Badejo yace; kirkirar wannan Ma'aikata ta makiyaya zai kawo saukin rikici tsakanin Makiyaya da Manoma.

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah yayi kira ga Gwamnatin tarayya da ta sanya mutanin kirki da zasu jagoranci wannan Ma'aikatan, saboda makiyaya zasu amfana.

Yace; Gwamnat ta duba da kyau kada ta dauko mutanin da zasuyi amfani da wannan Ma'aikatar su azurta Kansu. Su kyale makiyaya cikin wahala. Ya zama rijiya tabada ruwa guga ta hana.

Alhaji Bello Badejo yace; yanzu  ya lura kowa na kokarin danganta kansa a matsayin shugaban Fulani.

Yace; Tsohon Gwamna da Tsohon Sanata da Sarakuna yanzu kowa na kokarin danganta kansa da shugabancin Fulani.

Da aka tambayeahi ko Kungiyar Fulani ta shirya shiga Zanga zangar da ake kokarinyi a qasa?

Bello Badejo yace; Fulani basu da wannan kuddurin domin matsalolin da yake daminsu kadai ya ishesu.

Yace; Fulani sunyi bakin jini a Najeriya komai ya faru mara kyau sai ace fulani.

Badejo yace; jihohi irin Katsina da Zamfara da Sokoto Fulani sun zama saniyar ware, ana musguna masu.

Yace; hakika kungiyar Fulani ta Miyatti Allah bata goyon bayan ta'addanci. Duk Wanda yayi lefi a hukuntashi. Amma bai kamata ace anayiwa Fulani kudin goyo ba.

Yace; bai kamata ana kai hari kan mai uwa da wabi ba. Ana kashe mai lefi da mara lefi.

Sannan yayi kira ga Gwamnatochin jihohin da surikayiwa Fulani adalci tunda ana zaman tare.

Haka zalika ya bukaci Gwamnoni suyi koyi da Gwamnan jihar Nager da ya kirkire Ma'aikatan kiwo a jihan shi.

Da aka tambayeshi game da dokar da Gwamnatin jihar Benue ta kafa na hana kiwo a bayyane.?

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah yace; a baya jihar Benue ta samu shedanin Gwamna wanda baya son zaman lafiya ya haddasa fitintunu tsakanin kabilar Tibi da Fulani. Amma yanzu Allah ya kawo Gwamna mai kaunar mutani mai son zaman lafiya a Benue, Fulani suna jihar suna kiwo babu wani takura.

Badejo ya godewa Shugabannin kungiyar Fulani ta Miyatti Allah ta jihohi da suka ziyarceshi sukayi adu'ar Allah ya kiyaye irin iftila'in da ya faru da shi a kwanakin baya.

No comments