Kungiyar Likitocin Kwakwalwa Masu Neman Sanin Makamar Aiki (Association of Resident Doctors ) Kware Chapter, sun yi Kira ga Gwam...
Kungiyar Likitocin Kwakwalwa Masu Neman Sanin Makamar Aiki (Association of Resident Doctors ) Kware Chapter, sun yi Kira ga Gwamnati da Hukumomi Najeriya da Su Taimaka Su Sa Hannu Domin Kubutar da abukiyar aikinsu dake Hannun Masu Garkuwa da Mutane Tsawon Wata 7.
Doctor Ganiyat Wadda aka Dauka a Cikin Gidanta dake Asibitin Idanu na kaduna Tun Watanin baya.
Shugaban Kungiyar Likitocin Yankin Kware Doctor Zubairu Umar Gidan Madi cikin wata ganawa da yayi da Manema Labarai yayi kira ga Al'umma da Su Taimaka da Adu'a da kuma bada Gudumuwa Domin ganin Kubutar wannan Boyar Allah
Sakataren Kungiyar Doctor *Hamza Umar Gado* Yayi Allah wadai da Faruwar Irin Wadannan Abubuwa acikin Kasa, Inda Yayi Kira ga Jami'an Tsaro da Sukara Kaimi Wurin Samar da Tsaro ga Al'umma....Cue Doctor
Doctor *Fatima Idiris Abdulmalik* Babbar Likita a Asibitin Kulawa da Kwakwalwa ta Kware Tayi Nuna tausayinta Sosai ga Wannan Abukiyar aikin Tasu *Ganiyat* inda ta roka ataimaka adawo da ita cikin Iyalanta Matsayinta Uwa Macce. Cue In....
Lamarin Tsaro Dai Naci gaba da Tabarbatewa a Arewa Maso Yammacin Najeriya, Duk Kokarin Da Gwamnati keyi Na ganin Ta Kauda Matsalar.
Aishatu Muhammad Bello Taskira Asirin Mai Daki
No comments