Inji Madakin Kwandare Daga Zubairu Lawal Madakin Kwandare Alhaji Muhammadu Abubakar Maikwarya yayi alkawarin hadakan da kawo c...
Inji Madakin Kwandare
Daga Zubairu Lawal
Madakin Kwandare Alhaji Muhammadu Abubakar Maikwarya yayi alkawarin hadakan da kawo cigaba da tabbatar da zaman lafiya a Kwandare.
sabon Madakin Wanda Masarautan Kwandare dake karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa ta nada a ranar Asabar ya taabbatar da samar da hadinkai da zaman lafiya ga al'umman Kwandare.
Alhaji Muhammadu Abubakar Maikwarya yace; duk kabilun Dake zaune a masarautan Kwandare masoya junane suna da kyakyawar fahinta a tsakaninsu.
Fhintar juna da zaman lafiya yasanya Sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Al-makura yayi nadin sarauta ga Qabilu dabam dabam domin kara tabbatar da zaman lafiya.
Madaki yace; duk cikansu da aka basu wannan sarautan zasu kara hadakai wajen bada shawarwari na cigaban wannan masarautan da al'umman Kwandare.
Yace; hadin kansu da shawarwarinsu zai kara tabbatar da zaman lafiya.
Taron da ya gudana a garin Kwandare ya samu hakartan manyan baki da masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya.
Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya Madakin Kwandare shine Shugaban kungiyar durebobin sufuri ( NURTW) ta jihar Nasarawa.
Kafin nadinsa a matsayin Madakin da farko shine Bunun Kwandare.
Masarautan Kwandare ta nada
1. Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya Madakin Kwandare.
2.Oboshi Jarmai - Jarman Kwandare
3. Alhaji Ibrahim Adahama. Sarkin padan Kwandare.
4. Aliyu me gida Abubajar Danmasanin Kwandare.
5.Abdul Ahmad Kura, Danllatun Kwandare
6.Muhammad Moyi Barde. Yariman Kwandare.
7.Muhammad .adaki sarkin pada karami.
8. Al-makra sarkin dawaki
9. Sulaiman Agyo . Jarumin Kwandare
10. Faisal Ahmad Al-makura Garkuwan Kwandare.
11.Nasiru Kasimu, Shattiman Kwandare.
12. Mudir Ahead Al-makura bunun Kwandare.
13. Me adisi Zannzan Kwandare.
14. Sulaiman Osuba Sarkin dawakin mai tuta.
15. Gwani Iman Aliyu, Shattiman Ilumun Kwandare.
16.i20sma'ila yahuza sarkin unguwan azaran Kwandare.
17.Aminu musa Baradan Kwandare
18. Yakubu Abdullahi Galadima. Fakacin Kwandare.
19. L.C. Nasiru Al-makura. Sarkin yakin Kwandare.
20. Idiris Abubakar Hardon fulanin Kwandare.
No comments