Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

ZA MU KAFA DOKAR HANA MATASA YIN D.J DA SAURAN BADALA.

~Sarkin Kafin madaki. Daga:Alh.lawal k.madaki. alhajilawalkm@gmail.com A ranar Talata 4/2/2025 ne fadar mai girma sarkin kafin m...

~Sarkin Kafin madaki.

Daga:Alh.lawal k.madaki.
alhajilawalkm@gmail.com

A ranar Talata 4/2/2025 ne fadar mai girma sarkin kafin madaki da ke karamar hukumar Ganjuwa Jihar Bauchi, ta kira taron masu rike da sarautun gargajiya, Malamai, shugabannin da "Yan kasuwa da ke karkashin gundumar ta kafin madaki fadar Mulkin Karamar hukumar ta Ganjuwa, domin neman hanyoyin da za'a bi don magance matsalolin tarbiyyar Matasan yankin.
Taron Wanda ya hada da shugabannin tsaro da suka kunshi Jami'an "Yan Sanda, Civil Defence, SS Tare da kungiyoyin Sintiri ("Yan sa Kai) A lokacin taron an tattauna matsaloli da dama da suka shafi gurbacewar tarbiyyar Matasa a yanki.
Almizan ta tuntubi Sarkin Kafin madaki Alhaji Sulaiman Adamu domin Ji daga gareshi, Sarkin ya yi wa Almizan Karin haske da ce wa; Tabbas ya kira wannan taro ne na masu Ruwa da tsaki a karkashin masarautansa sakamakon korafe-korafen talakawasa akan lalacewar tarbiyyar matasa.
Daga cikin dokokin da suka gabatar sun hada da Hana kidan D.J da Matasa ke yi lokacin bikin Aure, sai yawan ganganci da ababen hawa, Since salansar Babura, munanan Aski da shauran abubuwan da suke bata tarbiyya. Sannan daga cikin dokokin akwai Haramta safarar karnunaka da Matasan ke yi Wanda haka ya saba wa Addininmu da al'adunmu ya jaddada.
Ko da Almizan ta nemi jin ko wani shiri su ke yi domin inganta rayuwar Matasan, sai ya Kara da ce wa; shi yasa suka Sanya Malamai da masu hanu da shuni cikin lamarin. Dangane da matsalar yaran "Yan siyasa Kuwa sarkin ya ce lallai shi yasa suka rubuta takarda zuwa fadar Hakimi daga nan Kuma za'a tura gaban shugaban Karamar hukuma domin neman hadin kansu ta yadda ko ta shafi yaran "Yan siyasa ba za su yi mana katsalandan ba.
Daga karshe sarkin ya yi kira ga al'ummarsa da su bada hadin Kai wa wannan kudiri domin inganta tarbiyyar Matasa, tare da yin kira ga takwarorinsa na shauran yankuna da su ma su yi koyi da wannan tsari don samar da ingantacciyar zaman lafiya a kasa.

No comments