Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

GWAMNAN ZAMFARA YA YI ALHININ RASUWAR ALMAJIRAI 17

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna alhinin sa bisa ibti'in gobarar da ta yi sanadiyyar rasuwar wasu almajirai 17 a ji...

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna alhinin sa bisa ibti'in gobarar da ta yi sanadiyyar rasuwar wasu almajirai 17 a jihar. 

A Æ™alla wasu almajirai 17 ne suka rasa rayukan su a wata makarantan allo da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda sakamakon wata mummunar gobara. 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu  Larabar nan, ya bayyana cewa Gwamnan ya nuna wannan ibtila'i a matsayin abin takaici. 

Sanarwar ta ambota Gwamna Lawal yana cewa, "Na kaɗu matuƙa da jin gobarar da ta tashi a makarantar Malam Ghali, wata makarantar almajirai da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.

“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina miÆ™a ta'aziyyar mu ga iyalai, makaranta da ma dukkan Æ™asar nan baki É—aya bisa wannan rashi na waÉ—annan yara. 

“Ina addu'ar Allah MaÉ—aukakin Sarki ya Æ™ara wa iyaye da 'yan uwan waÉ—annan yara haÆ™urin jure wannan rashi. Ina kuma addu'ar Allah ba waÉ—anda ke kwance a asisibi lafiya. 

“A matsayin gwamnatin mu mai sanin ya-kamata, za mu yi nazari domin gano musabbabin wannan gobara don a É—auki matakan kare aukuwar lamarin nan gaba. 

“Za mu bayar da duk gudumawar da ta wajaba ga iyalan waÉ—anda abin ya shafa."

No comments