Daga Hussain Yero Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Katsina, Jamiyyar APC ta Kaddamar da "yan takarar Kamsiloli da Shugaban K...
Daga Hussain Yero
Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Katsina, Jamiyyar APC ta Kaddamar da "yan takarar Kamsiloli da Shugaban Karamar Hukuma da mataimakin sa,a Maskan cikin Karamar Hukumar Funtuwa Jihar Katsina.
Masu ruwa da tsaki na Jamiyyar APC da masu mukaman Siyasa ne suka Jagoranci Kaddamar da Kamfendin a garin na Maska.
Da ya ke bayani Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon Musa Adamu Funtua, ya bayyana cewa,sunzo tushen Funtuwa watau Maska dan neman albarka na Kaddamar da Kamfendin Neman nasarar zaben Kananan Hukumomi da Hukumar Zaben Mai zaman kanta ta Jihar Katsina zata gudanar a ranar 15/02/2025.domin sake zaben 'yan kararmu na Jamiyyar APC baki daya".
" Hon Musa Adamu ya kuma tabbatar da cewa,zabubukan da suka gabata da al'ummar jihar Katsina suka zabi Jamiyyar APC sun tabbatar basuyi zaben tumun dare ba.sunga ayyukan da mai girma gwamnan Katsina Malam Dikko Rada ya ke zubawa a fadin Jihar ta Katsina.kuma an dauki ma'aikata da kuma turo 'yan jahar Katsina karo karatun a jami'oin wajen kasar nan musammam ma'aikatan lafiya dan kula da lafiya al'ummar Jihar Katsina.
Akan haka ne muke mika kokon bararmu ga alummar Karamar Hukumar Funtuwa da na jihar Katsina baki daya da su sake zaben 'yan takarar mu dan cigaba da ayyukan more rayuwa ga alummar.
Da ya ke gabatar da 'yan takarar,Jigon A Jamiyyar APC Hon Shamsu Sule ya kalubalanci wani jigo a Jamiyyar adawa inda ya bayyana cewa,sun shirya tsaf wajan fafatawa da duk wani mai ja da gwamnatin Dikko Rada a fadin Jihar Katsina,kowa wanene. kuma Ina kira gareshi da yaja bakin sa yayi shiru idanko ba haka ba, lallai zamu fasa kwai al'ummar Jihar Katsina su tabbatar da cewa,makiyinsu bama soyin suba.
Dan majalisa tarayya, mai wakiltar Kananan Hukumomin Funtua Dandume a Majalisar Wakilai,Hon Abubakar Gardi ya baje kolin ayyukan da yayima alummar mazabar sa Funtua Dandume,akan haka ne shima ya ke rokon kuri'ar su ga 'yan takarar su na Shuganin Kananan Hukumomi da Kamsiloli a zaben mai zuwa.
Shima Anas Jawabin Dan Majalisar Jihar Katsina,Hon Abubakar Total ya bayyana cewa,duk 'yan takarar su babu bara gurbi dan haka duk Wanda aka zaba lailai zasuyi abunda ya kamata na cigaban Karamar Hukumar Funtuwa.
Shugaban Hukumar Amsar Haraji na jihar Katsina kuwa , Alhaji Aminu Isyaku ya bayyana cewa, ayyukan da gwamna Radda ke yi a Karamar Hukumar Funtuwa da Jihar Katsina baki daya na cigaban alumma ya kamata muduba mu zabi 'yan takarar Jamiyyar gwamna Radda ta APC a zaben Kananan Hukumomi da za'a gudanar a ranar 15/2/2025 .dan nuna godiya ga reshi .
Sanata Muntari Dan Dutse ya bayyana ayyukan da ya kawo a yankin Funtua daga gwmanatin tarayya na cigaban alumma,da kuma ayyukan da gwamna Umar Dikko Rada keyi ya sanya jiga-jigan Jamiyyar Adawa ta PDP a Funtua ya amshesu zuwa Jamiyyar APC sabo da sunga aiki a Kasa ba yaudara ba inji Sanata Dan Dutse.
"Wannan na tabbatar da cewa,muke da na sara a zabe.mai zuwa da yardar Allah.
Akarshe amdadin 'yan takarar Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa,Hon Abdu Goya ya bayyana godiyar su ga Jamiyyar APC ta zabo su a zaben Kananan Hukumomi da yardar Allah idan muka kai gaci ba zamuba jama'ar mu kunyaba.zamuyi koyi da gwamna Umar Dikko Rada wajan ayyukan cigaban alumma.
No comments