Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Rukunin Sakatariyar Jihar Zamfara Da Aka Gyara, Ya Ce Ba A Samar Da Ababen More Rayuwa Kawai Gwamnatinsa Za Ta Tsaya Ba

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa burin gwamnatinsa na sake fasalin ayyukan gwamnati ya wuce samar da ababen mo...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa burin gwamnatinsa na sake fasalin ayyukan gwamnati ya wuce samar da ababen more rayuwa kaɗai.

Gwamnan ya ƙaddamar da ginin ‘C’ da aka gyara na rukunin sakatariyar JB Yakubu na jihar da ke Gusau a ranar Laraba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ginin da aka gyara na ‘A’ na rukunin sakatariyar an ƙaddamar da shi ne tun watan Mayun bara.

A jawabinsa a wurin bikin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa taron ba wai kawai ƙaddamar da wani gini ne da aka gyara ba, har ma da jajircewar gwamnatinsa na inganta ayyukan gwamnati da samar da yanayin aiki mai kyau ga ma’aikatan jihar Zamfara.

Ya ce, “Na tuna cewa a shekarar da ta gabata ne muka taru a nan domin ƙaddamar da ginin ‘A’ da aka gyara, a yau cikin yardar Allah (SWT) mun miƙa wa jama’a ginin “C” domin yi wa jama’a hidima, In Sha Allah, nan ba da jimawa ba za mu koma ginin B, inda daga nan ne za mu kammala gyaran dukka sakatariyar.

“Waɗannan gine-ginen da aka gina sama da shekaru ashirin da suka gabata, sun tabarbare sosai sakamakon rashin kula da su na tsawon shekaru, bayan da muka hau mulki a shekarar 2023, mun ba da fifiko wajen gyara waɗannan muhimman gine-gine a matsayin wani bangare na ƙoƙarin da muke yi na sabunta kayayyakin aikin gwamnati.

“A yau, muna shaida sakamakon wannan alƙawari, tare da ƙaddamar da wani katafaren ofis da aka gyara, da cikakkun kaya, da kuma katafaren ofis wanda ya cika ƙa’idojin aikin gwamnati na zamani.

“Burinmu na sake fasalin ayyukan gwamnati ya wuce samar da ababen more rayuwa, mun yi imanin cewa ma’aikaci mai ƙwazo da ƙwarewa shi ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari, shi ya sa a ƙarƙashin gwamnatinmu muka warware matsalar basussuka da muka gada daga gwamnatocin baya na sama da Naira Biliyan 13, hakan ya kawo biyan haƙƙin manyan mu da suka yi wa jihar nan hidima.

“A ƙoƙarinmu na neman shugabanci nagari, mun gabatar da jarrabawar farko a tarihin jihar Zamfara ga daraktoci masu neman muƙamin Babban Sakatare, ta hanyar wannan tsari ne muka naɗa Manyan Sakatarori guda goma sha biyu bisa cancanta, ta haka ne muka kafa harsashin samar da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati da gasa.”

Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da bin tsarin biyan fansho a kowane wata domin hana galabaitar waɗanda suka yi ritaya daga Zamfara.

"Haka kuma mun ƙara faɗaɗa ayyukan jin daɗin ma'aikata ta hanyar gabatar da wani garabaras na ƙarshen shekara, wanda aka fi sani da "albashin wata na 13" Ma'aikatan gwamnati ba su taba samun wannan ba tun lokacin da aka kafa jihohi.

No comments