Daga Bello Hamza, Abuja Lokacin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Kasa karo na 102 ta yanke shawarar war...
Daga Bello Hamza, Abuja
Lokacin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Kasa karo na 102 ta yanke shawarar ware takarar shugaban qasa na shekarar 2027 ga Kudu, yanayin siyasa a kasar ya dauki zafi tare da dimbin ce-ce-ku-ce kan wane ne zai dauki tikitin babbar jam’iyyar adawa a Afirka.
Masu sharhi kan siyasa da wasu masu adawa, musamman daga jam’iyyar mai mulki ta APC, tun da farko sun yi gaggawar cewa PDP ta mutu kuma ta shirya zuwa makabarta. Sai dai abin mamaki, jam’iyyar da ake ganin ta mutu ta sake tashi, inda ta ayyana watan Nuwamba a matsayin lokacin da za ta gudanar da babban taron zaben shugabanni a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Zaben Ibadan a matsayin wurin gudanar da babban taron PDP ya haifar da fargaba musamman a cikin sansanin jam’iyya mai mulki, game da abin da ka iya kasancewa sakamakon babban zaben 2027 idan PDP ta tsara komai yadda ya kamata.
Wannan fargaba ba ta tsaya ga jam’iyyar APC kadai ba, har ma da wasu manyan jiga-jigai a cikin PDP da suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu na APC abin da da dama suka kira babbar hujja ta korarsu daga jam’iyyar, yanzu sun fara jin tsoron sabuwar PDP da ke tasowa.
Wasu masu nazarin siyasar Nijeriya sun bayyana ayyukan cin amanar jam’iyya da ke gudana a PDP a matsayin abin da bai taba faruwa ba tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999. Amma yayin da PDP ke kokarin sake farfadowa don shirye-shiryen manyan zabuka masu zuwa, sabon yanayin da ya kunno kai ya sa aka fara tambayar nan mai muhimmanci. Wanene ke tsoron Seyi Makinde, Gwamnan Jihar Oyo?
Idan aka yi xan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba daya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne dan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027.
Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake kira da “Star Boy”, ya kafa kansa a matsayin jagoran PDP a yankin yamma, tafiyarsa zuwa kujerar gwamna ba ta zo masa da sauki ba.
Kafin shekarar 2019, Makinde ya tsaya takarar kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a shekarar 2007, amma ya sha kaye a hannun Kamoru Adedibu. Duk da wannan rashin nasara ta farko, bai karaya ba. A 2010, karkashin jam’iyyar PDP, ya sake neman kujerar Sanata na Oyo ta Kudu a zaven 2011, amma ya sha kaye a zaben fid da gwani a hannun sanatan da ke rike da kujerar a lokacin.
A 2014, Makinde ya nemi tikitin PDP domin takarar gwamnan Jihar Oyo a zaven 2015. Amma a watan Disamba 2014, bayan kammala zaben fid da gwani, jam’iyyar ta hana shi samun tikitin gwamna. Duk da haka, Makinde ya ci gaba da jajircewa bisa burinsa na yi wa al’ummar Oyo hidima, yana mai dagewa kan hangen nesansa na ci gaban jihar.
A ranar 29 ga Satumba 2018, Makinde ya zama xan takarar gwamna na PDP a babban zaven 2019 a Jihar Oyo, bayan ya samu kuri’u 2,772 a zaven fid da gwani. Kamar yadda ya bayyana a lokacin: “Mutanen Oyo ne suka yanke shawara a 2019. Ba mu da wani uba a siyasa. Babu wanda ya dauki nauyinmu. Babu wanda ya ba mu ko sisin kobo don mu kai ga nasara.”
Yau, Makinde ya shafe sama da shekaru shida daga cikin shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya amince masa ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Oyo. Ko da yake bai bayyana niyyarsa game da 2027 ba tukuna, tursasawa da kira gare shi da ya shiga fagen takarar na kara karfi a kullum.
Masu nazarin siyasa na ci gaba da sa ido kan matakan da zai dauka a nan gaba yayin da wa’adin gwamnatinsa na biyu ke gab da karewa. Wata makoma ce da dama a cikin jam’iyyar mai mulki, da ma wasu daga cikin PDP, ke ganin abin tsoro ne da damuwa.
A 2019, Makinde bai dogara da wani uban gidan siyasa ba, amma ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Oyo. A yau kuma, mutane da dama a fadin kasar na ganin cewa, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027, akwai yiwuwar ya maimaita irin “sihirin nasara” da ya yi a Oyo.
Da yawa na ganin cewa dama tana gefensa daga zaben fid da gwani na PDP har zuwa babban zaben shugaban kasa a 2027. Ko da yake bai fito fili ya sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ba tukunna, amma shahararsa da ke kara bunkasa a cikin PDP da wajenta, na nuna irin karbuwar da yake samu a matakin kasa, wanda ya sa ake kallonsa a matsayin babban kalubale ga duk wani dan takarar APC a gaba.
Gwamna Makinde, sabanin wasu a cikin jam’iyya, ya tsaya tsayin daka kan akidar PDP, ya tsaya tare da jam’iyyar a lokutan kalubale.
A lokacin da manyan jiga-jigan PDP suka gudu suka koma APC da sunan neman haduwa da “cibiya mai karfi”, Makinde bai bar jam’iyyar ba, maimakon haka ya tallafa mata da dukiya da albarkatu.
A yau, farin jinin Gwamna Seyi Makinde ya kai kololuwa, yana ratsawa cikin dukkanin shiyyoyin kasar shida. Wannan ya sanya jam’iyyar mai mulki cikin fargaba, yayin da salon jagorancinsa ke kara yin karfi har zuwa wajen nahiyar Afirka.
An gwada farin jinin Gwamna Makinde a ranar 16 ga Agusta, 2025, lokacin da aka gudanar da zaben cike gurbi na majalisar tarayya a Ibadan North Federal Constituency. Dan takarar PDP, Fola Oyekunle, ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 18,404, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Adewale Olatunji, wanda ya samu kuri’u 8,312.
An gudanar da wannan zabe ne domin cike gurbin rasuwar Hon. Olaide Akinremi ta bari.
Sakamakon ya nuna nasara mai karfi ga PDP a Jihar Oyo karkashin jagorancin Gwamna Makinde, tare da zama shaida kan tasirinsa da kuma gagarumin farin jininsa a jihar, abin da ke sa abokan hamayyarsa a fagen siyasa cikin fargaba.
A ‘yan kwanakin nan ma, wata kungiyar masu goyon bayan PDP mai suna Reset Lagos PDP ta yi kira ga al’ummar Inyamurai (Igbos) a fadin kasar da su hada kai wajen mara wa Gwamna Makinde baya domin ya karbi mulki a shekarar 2027.
Mai shirya kungiyar, Dr Adetokunbo Pearse, wanda shi ma shugaban National Support Group for Makinde ne, ya shaida wa manema labarai cewa Makinde ya bambanta da sauran masu sha’awar takara, kuma yana da gaskiya da sha’awar ci gaban al’ummar Igbo a zuciyarsa.
Ya ce, “Shi ne kadai ya nuna sha’awa a tsayawa takara, kuma ya yi bajinta sosai a matsayin gwamnan Jihar Oyo. Ya shiga siyasa ba tare da dogaro da kudin gwamnati ba, tun daga jami’a, sabanin yawancin ‘yan siyasa da ke shigowa da komai a hannunsu sannan su fara dogaro da dukiyar gwamnati.”
A gefe guda, shugaban reshen Legas na Igbonine Great Peoples Assembly, Elder Okezie Anyanwu, ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai kasance yadda aka saba ba, inda ya yi kira ga Inyamurai da ke Legas da su hada kai da PDP, wacce ya bayyana a matsayin jam’iyya mai ingantattun tsare-tsare a Legas.
Ya ce, “Dalilin da ya sa na ke tare da PDP shi ne ita ce kawai jam’iyya da ke da tsari a kowane sashi na Nijeriya. Kuma tubalin PDP ya ta’allaka ne kan nagarta da gaskiya sabanin wadannan jam’iyyun da suka fito daga baya. Ina kira ga kowa da kowa da ya kada kuri’a yadda ya dace.”
Idan za a iya tunawa wata kungiya mai suna ‘Nigeria Youths Awareness Group Makinde 2027’ (NYAG Makinde 2027), a watan Mayu, yayin taron manema labarai a Kano kan hasashen siyasar zaben shugaban kasa na 2027, ta bayyana a fili cewa tana alfahari da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin mutumin da zai iya ciyar da Nijeriya gaba.
Kungiyar ta bayyana cewa dukkanin ‘yan Nijeriya masu kishin dimokuradiyya ya kamata su hada kai a bayan Makinde ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, domin tabbatar da samun tikitin tsayawa takara.
Yayin ganawa da manema labarai a Kano, Alhaji Lawal Abdullahi, Sakataren Kasa na kungiyar, ya bayyana cewa: “Mun hadu a matsayin kungiyoyi daban-daban kuma mun amince mu yi tafiya tare domin Seyi Makinde ya zama shugaban kasa a 2027. Mu jirgin da ke tafiya ne, babu wani abu da zai iya tsayar da mu sai mun cimma burinmu na shugabancin Seyi Makinde.”
Gwamna Seyi Makinde tun da farko ya kasance mai jituwa da Arewacin kasar nan a harkokinsa na siyasa, tattalin arziki da kuma zamantakewa. A lokacin da rikicin jam’iyyar PDP ya yi tsanani, Makinde a tattaunawarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar daga Arewa ya taka rawar gani wajen sasanta al’amura domin kubutar da PDP daga rugujewa.
Makinde bai tava boye matsayinsa kan batutuwan jam’iyya ba. Yayin hira da ‘yan jarida kwanan nan bayan taron tunawa da cikar shekara 10 da naxin Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi, ya yi tsokaci kan ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Qasa, Atiku Abubakar, daga PDP. Ya ce: “Siyasa wasa ne na muradu.
Ban yi imani cewa ficewarsa zai bar wani gibi ga PDP a matsayin jam’iyya ba. PDP wata kungiya ce mai karfi. Muna da ‘yancin shiga da fita. Duk wanda yake riqe PDP da hannunsa, gara ya fice.
Abin da ya kamata mu fahimta shi ne: ‘yan wasa suna zuwa suna tafiya, gwamnoni suna zuwa suna tafiya, shugabanni suna zuwa suna tafiya, amma jiharmu da qasarmu za su ci gaba da wanzuwa.”
A nasa bangaren, Hon. Dare Adeleke, wanda shi ne mai ba wa Gwamna Makinde shawara kan harkokin Mazabu na Tarayya, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki APC na cikin firgici da tasirin Makinde a siyasar kasar kafin 2027.
Adeleke ya ce: “APC na cikin tsananin tsoro da yiwuwar tikitin Makinde a karkashin PDP. Sun san cewa idan ya tsaya takara, hakan na iya zama mummunan hasashe ga mulkinsu mai cike da gazawa, mulki da ake iya cewa shi ne mafi ban takaici a tarihin Nijeriya.”
Shaharar Makinde a fadin kasar ta zama babban kalubale ga wadanda ya doke sau biyu a Jihar Oyo. Suna fargabar cewa zai maimaita irin wannan nasara idan ya shiga fafatawar shugaban kasa a 2027.
Ga jiga-jigan PDP da ke da wannan ra’ayi, Gwamna Makinde na da kwarewa da cancantar da za su iya kai jam’iyyar ga nasara a babban zaben 2027.
Yayin da tafiyar 2027 ke qara bayyana a fili, ‘yan Nijeriya na jiran ganin fitattun ‘yan siyasa sun fito da kundin ayyukansu da zai nuna irin mulkin da suka yi da kuma abin da za su iya kawowa.
No comments