Daga Muhammad Sakafa, Kano msakafa@gmail.com Wannan Kiran ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar mabiya da masoyan Ahlul bait...
Daga Muhammad Sakafa, Kano
msakafa@gmail.com
Wannan Kiran ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar mabiya da masoyan Ahlul bait (as) ta kasa reshen jihar Kano wadda aka fi sani da AHLUL BAITI NAJERIYA, Hon. Adamu kabiru (Auduwa) a zantawar da yayi da manema labarai a Kano.
Honourable Adamu kabiru ya Kara da cewa " muna Kira da dukkan mabiya da masoyan Ahlul bait na kasar nan da su dukufa wajen zuwa yankar Katin rijistar zabe don samun damar Kada kuri'a a dukkan matakai na zabuka masu zuwa.
Shugaban na gamayyar ya Kara da cewa "wannan wata dama ce a yanzu na fitowar dukkan mabiya Ahlul baiti don yankar Katin zaben duba da irin yawan adadin da muke da su na mabiya na Ahlul bait (as) a Fadin kasar nan, ganin yanzu aikin yana Kan gudana a dukkan ofisishin zabe na dukkan kananan hukumomin 774 na Fadin kasar nan, don haka dukkan Wanda ya San bashi da Katin zaben a baya ko kuma ya bata ko matasan da a shekarun da aka yi aikin Katin zaben shekarunsu Basu Kai ba, Amma yanzu shekarunsu sun Kai mazansu da mata da su gaggauta yankar Katin zaben su Adana Shi zuwa lokacin zabuka masu zuwa Wanda zuwa lokacin ne za'a ji matsayarmu ta Wanda zamu kadawa kuri'unmu Wanda Zai Kare mana mutumcinmu da fahimtarmu ta addini da kuma wasu hakkokinmu da kowanne Dan kasa ke da Shi Wanda kundin tsarin Mulkin kasar nan ya bamu". Inji Shi.
Haka nan Hon. Adamu kabiru ya Kara da cewa "babu wani mai mukami ko mai neman mukami a yanzu da ya bamu wani abu don muzo mu sanya mabiya su yanki wannan Katin rijistar ta zabe, Amma abinda ya kamata a sani shine ko Mai yawan kuri'un da muka yanka zamu kadawa wani dan takara ne, to Amma wanne irin dan takara zamu kadawa? Wannan Shi yakamata a sani, to a matakin farko shine sai mu duba wanne irin dan takara al'umma suka fi ganin cancantarsa a zaben? Don mu ba wani Abu dabam muke bukata ba Sama da na al'umma a'a zamu duba wanene aka fi kyautata masa zaton da Kare hakkokinmu, don haka muna sanar da mabiya cewa zuwa yanzu babu wata jam'iyya ko Dan takarar da muka tsayar zamu zaba zuwa yanzu har sai mun tsaya mun tantance ta hanyar zame zame da tattaunawa da malamanmu da mufakkiranmu domin haduwa waje Daya don tunkarar Dan takara ko jam'iyyar da ta dace mu yi". Daga karshe shugaban yayi Kira ga hukumomin kasar nan da su tabbatar cewa sun Baiwa dukkan wani Dan kasa damarsa da yancinsa Wanda kwansitushin din kasa ya bashi ba tare da sun tauuye masa hakkinsa na, haka nan ina Kira ga dukkanin mabiyan Ahlul baiti tare da dukkanin rabe rabenmu bangarorinmu cewa malamanmu sun wayar da dukkan mabiya a cikin najeriya Kan cewa duk Wanda ya cika ko ya Kai shekarun 18 ya yanki Katin kuri'arsa, haka su kuma sauran al'umma da su gane cewa tafiyar Ahlul baiti tafiya ce ta al'umma Baki daya babu wani bangaren na akida KO wata fahimta da muke kyama kuma alhamdu lillah a nan garin na Kano muna zaune lafiya da kowa."
No comments