Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

GWAMNA DAUDA LAWAL A SHEKARA 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

Daga Sulaiman Bala Idris Ba ni da kokwanto a kan cewa Dauda Lawal na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kwarjini a Nijeri...

Daga Sulaiman Bala Idris

Ba ni da kokwanto a kan cewa Dauda Lawal na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kwarjini a Nijeriya. Amma abu ɗaya da nake yawan samun ƙalubalen bayyana wa mutane shi ne shekarunsa.

Mutane sukan yi ihun 'kai!' wasu kuma su kan kalli idona cikin wasa da dariya su ƙaryata ni. Duk saboda na bayar da sahihin bayanin da na tabbata ɗari bisa ɗari a kan cewa Dauda Lawal zai cika 60 a ranar 2 ga Satumba, 2025 (wato yau).

Wani lokaci, nakan gaji da bayani. Ko da a ƙarshe sun yarda da shekarunsa, wasu mutane suna cusa musu shakku daga baya. Wasu suna nuna cewa ya bayyana a matsayin matashi kuma yana gyara kan sa ne saboda yana da dukiya.

Kun tuna jita-jitar da ake yaɗawa game wai arziƙinsa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma mutane da yawa sun gaskata.

A matsayinsa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantansa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakinsa sama da shekaru biyu.

A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al'umma.

Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da aka manta da ita zuwa babban birnin.

Dukkan abubuwan da mutane ke faɗi game da shi kama daga natsuwa, kamun kai, da tsabta daidai ne. Ya canja ɗabi’ar ma’aikata, musamman waɗanda ke gidan gwamnatin Zamfara, waɗanda ke aiki a kan kujerar mulki. Salon rayuwarsu ta canja, ba kamar da ba.

Gusau, babban birnin jihar, an gyara ta a matsayin cibiyar birane, kamar yadda ya kamata. An shimfiɗa titi tare da saka fitilu masu haske a ko'ina. Gusau, wacce ba ta da fitilun warware cunkoson ababen hawa a 2023 kafin zaɓe, yanzu haka tana da fitilun a duk faɗin birnin. Garin ya ƙawatu saboda a hankali ɗabi'un mutane yana canjawa.

A matsayina na mai fafutukar nuna ma’amala ta ƙwarai, ɗaya daga cikin manyan makarantun tunani na zamantakewar al’umma, na lura da yadda ƙa’idar ‘Kallo Ta Cikin Gilashi’ ta Charles Horton Cooley ke aiwatarwa a tafiyar Gwamna Dauda Lawal a Zamfara. Za ku iya cewa ta ya.

Kallo Ta Cikin Gilashi ra'ayi ne da ke bayyana yadda mutane ke yin tunanin kansu dangane da yadda suke tunanin wasu na fahimtarsu. Ta hanyar hulɗar zamantakewa, mutane suna amfani da maganganun wasu a matsayin "madubi" don tantance ƙimarsu, ɗabi'a, da halayensu.

A da, abin da mutane ke gani game da Zamfara idan suka kalli madubi, shi ne halin da ake ciki na ƙaƙani-ka-yi, jihar da ’yan bindiga da talauci suka kusa kawar da ita. Ita ce ƙarshe baya da fannin ilimi da kiwon lafiya. Dauda Lawal, masanin kimiyyar siyasa, ya canja wannan labari ta hanyar haɗa ƙa'idojin zamantakewa na aiki da ma'amala mai kyau.

Jihar Zamfara da mutane ke gani a madubi a yanzu, jiha ce da ke takara a matsayin jiha mafi inganci a fannin tattalin arziƙin cikin gida, ilimi, cibiyoyi masu tasowa, kiwon lafiya, da sauransu.

Aikin ceto na Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara, ba wai a Gusau, babban birnin jihar kaɗai ba.

Waɗannan manyan ayyuka sun shafi sassa daban-daban, waɗanda suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da sauran muhimman wurare masu.

Gwamna Lawal ya mayar da Babban Asibitin Anka zuwa wani katafaren asibiti na zamani mai ɗauke da na’urorin kiwon lafiya na zamani a ƙaramar hukumar Anka. An yi wa asibitin gyaran ciki da waje.

Gwamnatinsa ta kafa makarantar Tsangaya ta zamani a ƙaramar hukumar Gummi, makarantar da aka tsara don shigar da Almajirai cikin tsarin ilimi na zamani.

A ƙaramar hukumar Bakura, Gwamna Lawal ya gyara Kwalejin Kimiyyar Aikin Gona, tare da samar mata da kayan aiki, inda ya samar da damarmaki ga matasa don bunƙasa sana’ar 
su ta noma — ƙashin bayan tattalin arziƙin Zamfara.

A ƙaramar hukumar Bukkuyum, ya ɗaukaka darajar PHC Nasarawa Burƙullu zuwa babban asibitin zamani da na'urori na zamani domin amfanin al’ummar yankin. Bugu da ƙari, ya bayar da kwangilar gina titunan garin domin haɗa dukkan garuruwan da ke cikin ƙaramar hukumar.

Gwamna Dauda Lawal ya gyara babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Maru, tare da cikakken kayan aiki. Asibitin, wanda a baya ya yi fata-fata, yanzu an gyara shi yadda ya kamata.

A ƙaramar hukumar Talatar Mafara, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gina sabon babban asibiti, domin a halin yanzu asibitin ya lalace. Sauran ayyukan a Talata Mafara sun haɗa da gyare-gyare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara.

A ƙaramar hukumar Maradun, Gwamna Lawal ya inganta tare da gyara babban asibitin Maradun, inda ya mayar da shi Cibiyar Kula da Lafiya ta Zamani mai ɗauke da duk wasu kayayyakin jinya na zamani. Ya kuma gyara babban asibitin Maru tare da samar da na'urori na zamani.

Haka zalika, a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda, Gwamna Lawal ya gyara babban asibitin garin, tare da samar da kayan aiki, ya gina makarantar Tsangaya na zamani, ya kafa cibiyar koyar da sana’o’i da ta dace domin samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma gina ƙarin gidajen kwana a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ƙaura Namoda.

A ƙaramar hukumar Shinkafi, Gwamna Lawal ya amince da sake gina babban asibitin Shinkafi da kuma aikin sake gina makarantar Attahiru Bafarawa.

A Ƙaramar Hukumar Tsafe, Gwamna Dauda Lawal ya gyara babban asibitin Tsafe tare da samar da kayan aiki, ya kuma gudanar da gyaran gaba ɗaya na Makarantar Koyon Fasaha ta Tsafe, ya sake gina babbar tashar mota ta zamani ta Tsafe, da sake gina babbar kasuwa.

A Ƙaramar Hukumar Bungudu, Gwamna Lawal yana gina titin mahaɗa na Furfuri, titin Rawayya, aikin gyaran makarantar da aka amince da shi gaba ɗaya, da kuma aikin gyara da kayan aiki na makarantar sakandaren Ɗan Gwaggo.

Ina da abubuwa da yawa da zan faɗa, musamman game da dangantakar mutane da gwamna na. Na yi alƙawari zan yi shi a hankali, ba a lokaci guda ba. Yau rana ce da za a yi bikin mai nasara. Alhamdu lillah, barka da cika shekaru 60 ga mutum mai kyakkyawar zuciya. 

Barka da Ranar Haihuwa, Oga!

Sulaiman shi ne kakakin gwamnan jihar Zamfara.

Fassarar MAHDI MUSA MUHAMMAD

No comments