Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

MAULIDI: Gwamna Dauda Lawal Ya Taya Al'ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu'o'in Samun Zaman Lafiya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya. Gwamnan ya yi...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana cewa Musulmi na gudanar da bukukuwan Mauludin Annabi duk shekara a ranar 12 ga watan Rabiul Awal, wata na uku na Hijira.

“Gwamna Dauda Lawal a madadin al’ummar jihar Zamfara yana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

“Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).

“Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).

“Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.

“Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.

"Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta'addanci da duk wani nau'in aikata laifuka a cikin al'ummarmu."

No comments