Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal murnar cika shekaru 60 a duniya. Shugaba Tinubu ya ya...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal murnar cika shekaru 60 a duniya.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamnan bisa jajircewar sa na ci gaban jihar Zamfara da kuma jajircewar sa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 2 ga Satumba, 2025
Yayin da yake ba Gwamna Lawal tabbacin ci gaba da goyon bayan gwamnatin tarayya, shugaban ya ƙara ƙarfafa masa gwiwa da ya jajirce wajen ganin an samar da shugabanci na gari, da samar da haɗin kai, da samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.
“Gwamna Dauda Lawal, a madadin gwamnati da al’ummar Nijeriya, ina yi maka fatan samun ƙarin lafiya, ƙarfin gwiwa da hikima yayin da ka ke ci gaba da yi wa al’ummar Jihar Zamfara da ƙasa hidima,” inji Shugaba Tinubu.
No comments