Daga Yusuf Wali An gudanar da bikin Maulidin Manzon Allah (S), Sayyida Zahra (SA) da Imam Ali (AS) a garin Potiskum da ke jihar ...
Daga Yusuf Wali
An gudanar da bikin Maulidin Manzon Allah (S), Sayyida Zahra (SA) da Imam Ali (AS) a garin Potiskum da ke jihar Yobe, tare da raba kayan abinci ga al’umma.
Shaikh Abubakar Nuhu Talatar Mafara ne babban baƙon jawabi a wajen bikin Maulidin, yayin da Wakilin ’yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na yankin Potiskum, Malam Ibrahim Lawan ya gabatar da shi ga mahalarta taron.
Bikin, wanda ɗan’uwa Alhaji Muhammad Adamu (Alhaji Baba) ya shirya, ya gudana ne a harabar gidansa da ke Potiskum daga ranar Laraba zuwa Juma’a, 7 zuwa 9 ga watan Janairu, 2026.
An fara taron ne da karatun Alƙur’ani mai girma (Musaffa) a ranar Laraba, inda aka kwana ana gudanar da karatun a ranar farko ta taron.
A ranar Alhamis kuwa, an gabatar da Majalisin Mawaƙa, tare da jawaban malamai, inda Shaikh Abdullahi Hassan da Shaikh Abubakar Muhammad Baba suka gabatar da nasu wa’azozin, suna masu jan hankalin al’umma kan koyarwar Ahlul Baiti (AS) da muhimmancin koyi da rayuwar Manzon Allah (S).
A ranar kammala taron, wato Juma’a, ɗalibi Sa’idu Saƙafa Potiskum ya gabatar da Majalisi. Haka kuma, an raba kyautuka na musamman ga mutum 24, tare da rabon kayan abinci da suka haɗa da ƙananan buhunan garin masara da shinkafa, wanda adadinsu ya kai buhu 548.
Jama’a sun bayyana jin daɗinsu matuƙa da wannan tagomshi da suka samu albarkacin zagayowar Maulidin tsarkakan bayi. Sun yi fatan alheri ga Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky da kuma wanda ya shirya taron Alhaji Muhammad Adamu.
No comments