Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Jami’ar Kebbi Ta Karrama Gwamna Lawal Da Digirin Girmamawa, Ta Yaba Da Ayyukan Raya Zamfara

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Jihar Kebbi ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da digiri...

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Jihar Kebbi ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da digirin girmamawa na Dakta na Kimiyya (D.Sc Honoris Causa), a wani biki da ya ja hankalin jama’a.

An ba gwamnan wannan karramawa ne a ranar Asabar yayin bikin yaye ɗalibai karo na farko da jami’ar ta shirya a filin taro na jami’ar da ke Aleru, a Jihar Kebbi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Majalisar Gudanarwar Jami’ar ce ta amincewa da bai wa Gwamna Lawal wannan digiri na girmamawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an fara shirye-shiryen bikin yaye ɗaliban tun ranar Laraba da taron manema labarai da Shugaban Jami’ar, Injiniya Farfesa Danshehu Bagudu Gwandangaji, ya jagoranta.

Sanarwar ta ce, jami’ar ta bayyana cewa wannan karramawa na nuna ƙudurinta na girmama mutane da ayyukansu suka yi tasiri mai ɗorewa ga al’umma. Jami’ar ta ce ta bai wa Gwamna Lawal digirin Dakta na Kimiyya ne domin girmama gudunmawar da ya bayar wajen raya al’umma da kuma ayyukan ci gaba.
Majalisar jami’ar ta bayyana cewa nasarorin da gwamnan ya samu a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, gine-gine, tattalin arziki da walwalar ma’aikata su ne manyan dalilan da suka sa aka ba shi wannan karramawa. A cewarsu, irin waɗannan karramawa za su ƙara zuga gwamnan wajen ci gaba da jajircewa domin habaka Jihar Zamfara.

Tun da fari, Shugaban Jami’ar, Farfesa Bagudu Danshehu, ya bayyana cewa tun daga kafuwar jami’ar a shekarar 2005, ta riga ta yaye ɗalibai 7,221 a matakin digirin farko, tare da ɗalibai 669 na digirin digirgir, tsakanin zangon karatu na 2010/2011 zuwa 2023/2024.
Karramawar da jami’ar ta yi wa Gwamna Lawal na zuwa ne a wani lokaci da ake yaba wa gwamnatinsa bisa shirye-shiryen raya Zamfara da ke mayar da hankali kan walwalar jama’a da gina tubalin ci gaba mai ɗorewa.

No comments