Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

2027: Gwamna Lawal Ya Umarci Masu Riƙe Da Muƙamai Su Yi Murabus Idan Za Su Tsaya Takara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba da umarni ga dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha da ke da niyyar tsayawa takara...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba da umarni ga dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 da su yi murabus daga muƙamansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce wannan umarni ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Zaɓe da Shugaban Ƙasa ya rattaba wa hannu, tare da jadawalin zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya jagoranci zaman majalisar karo na 64, inda aka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jihar Zamfara.

A cikin jawabin buɗe taron, Gwamna Lawal ya jaddada cewa duk wani mamba na majalisar ko mai riƙe da muƙami da ke da burin tsayawa takara dole ne ya yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
Haka kuma, gwamnan ya umurci Sakataren Gwamnatin Jiha da ya fitar da sanarwa ga dukkan waɗanda aka naɗa a muƙaman siyasa da ke da niyyar neman zaɓe, domin su sauka daga kujerunsu kafin wa’adin da aka gindaya.

Bugu da ƙari, an umurci Shugaban Ma’aikatan Jiha da ya fitar da irin wannan sanarwa ga dukkan ma’aikatan gwamnati da ke da burin tsayawa takara, domin su bi ƙa’ida.
Gwamna Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yi wa al’ummar Zamfara hidima.

No comments