Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar farin cikinsa bayan nasarar gudanar da gwajin saukar jirgi na farko a sab...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar farin cikinsa bayan nasarar gudanar da gwajin saukar jirgi na farko a sabon Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa jirgin gwajin ya sauka da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, a wani lamari da aka bayyana a matsayin tarihi ga jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa jirgin da aka yi amfani da shi, nau’in Bombardier Challenger 605, mallakin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ne, wanda aka tura domin tantance inganci da shirye-shiryen filin jirgin kafin fara amfani da shi a hukumance.
A cewar sanarwar, wannan rana za ta kasance abin tunawa a tarihin Zamfara, kasancewar gwamnan ya shaida saukar jirgi na farko a filin jirgin da aka daɗe ana jira.
An bayyana cewa jirgin mai lambar rajista 5N-FGZ ya gudanar da gwaji na musamman domin tantance yadda filin jirgin zai iya karɓar manyan baƙi (VIP), musamman gabanin wasu muhimman zirga-zirga da ake sa ran yi a mako mai zuwa.
An kuma gudanar da wannan gwaji ne bisa tanade-tanaden dokokin sufurin jiragen sama na Nijeriya (Nigeria Civil Aviation Regulations), inda aka bi duk ƙa’idojin tsaro da aiki.
Kafin gudanar da gwajin, gwamnatin jihar ta nemi izini daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), wadda ta bayar da amincewa ta musamman wato No Technical Objection (NTO) domin saukar jirgin a Gusau.
Haka kuma, an gudanar da aikin jirgin ne bisa tsarin Visual Flight Rules (VFR), wanda ke nufin an yi zirga-zirgar ne a tsakanin fitowar rana zuwa faɗuwarta, kamar yadda ƙa’ida ta tanada.
Wannan gagarumin ci gaba ya ƙara ɗaga darajar gwamnatin Gwamna Lawal, musamman idan aka yi la’akari da cewa tun bayan kafuwar Jihar Zamfara sama da shekaru 30 da suka gabata, ba ta taɓa samun filin jirgin sama irin wannan ba.
No comments