Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar mai mulki ta APC. Cikin wa...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar mai mulki ta APC.
Cikin wata Sanarwar da ta fito a ranar Litinin cikin mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Nuhu Anka, ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan dogon tuntuba da shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a faɗin jihar Zamfara.
A cewar sanarwar, gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari mai zurfi kan halin da jam’iyyar PDP ke ciki da kuma buƙatar tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Zamfara.
Takardar ta bayyana cewa sauyin jam’iyyar ya zo ne bayan makonni na shawarwari da tattaunawa da shugabannin siyasa, dattawa, magoya bayan jam’iyya da kuma manyan jami’an gwamnati a jihar.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin jihar Zamfara tare da iyalan jam’iyyar PDP a jihar na sanar da jama’a wani muhimmin sauyi a fagen siyasa bayan tuntuba mai faɗi da shugabanni, dattawa da magoya baya a sassa daban-daban na jihar.
“Bayan zurfin tunani da nazari, kuma domin tabbatar da zaman lafiya, cigaba da ɗorewar ci gaban jihar Zamfara, gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa gwamnan ya ɗauki wannan mataki shi ne rikicin cikin gida da ya daɗe yana addabar jam’iyyar PDP a matakin ƙasa da kuma jihohi.
A cewar Nuhu Anka, rikice-rikicen shugabanci da matsalolin tsarin jam’iyyar da ba a warware ba sun haifar da rudani da kuma abubuwan da za su iya kawo tsaiko ga tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.
Ya ce irin wasannan matsaloli na iya hana gwamnati gudanar da ayyukanta yadda ya dace tare da kawo cikas ga isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar Zamfara.
Gwamnan ya kuma miƙa godiyarsa ga mambobin PDP a jihar Zamfara bisa goyon bayan da suka ba shi tun lokacin da yake cikin jam’iyyar.
Sai dai ya bayyana cewa halin da siyasar jam’iyyar ke ciki a halin yanzu ya tilasta masa daukar abin da ya kira “mummunan amma jarumtar mataki” domin amfanin jihar Zamfara.
A cewar mai taimaka masa kan yaɗa labarai, komawar gwamnan zuwa APC na da nufin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya wajen magance matsalolin tsaro da kuma hanzarta ayyukan ci gaba a jihar.
No comments