Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Halarci Taron Farko Na Liyafar Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya halarci taron cin abincin dare na farko da Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya halarci taron cin abincin dare na farko da Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa ta shirya, wanda aka gudanar a daren Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A yayin taron, Gwamna Dauda Lawal ya samu damar sanya wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lambar girmamawa ta Babban Majiɓincin Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa, wato Grand Patron of the State House Press Corps.
An shirya taron ne domin ƙarfafa alaƙa tsakanin 'yan jarida da manyan jami'an gwamnati, karrama waɗanda suka yi fice wajen bayar da rahotannin da suka shafi Shugaban Ƙasa, tare da samar da wata dama ta tattaunawa tsakanin kafafen yaɗa labarai da manyan shugabannin gwamnati cikin yanayi na sada zumunci.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci 'yan jarida su ci gaba da riƙon ƙwarewa, gaskiya, da ɗaukar nauyin abin da suke wallafawa.
Ya bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin muhimmin abokan hulɗa wajen gina ƙasa da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Shugaban ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta kare 'yancin aikin jarida da kuma 'yancin faɗar albarkacin baki kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.

Ƙungiyar 'Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙunshi 'yan jaridar da aka ba izinin yaɗa labaran Shugaban Ƙasa da dukkan ayyukan da ake gudanarwa a cikin Fadar Shugaban Ƙasa.

Taron na farko ya samu halartar Uwargidan Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; da Babban Ma'aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Ministan Kuɗi, Ministan Ilimi, Ministan Lafiya, Ministan Noma, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, da kuma Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack.


No comments