Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Bas-bas 50 Ga Ƙungiyar Direbobi Ta Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sabbin motocin bas-bas guda 50 ga reshen Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW) na jihar,...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sabbin motocin bas-bas guda 50 ga reshen Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW) na jihar, a wani mataki da gwamnatin ta ce na inganta harkokin sufuri da bunƙasa tattalin arziki.

An gudanar da bikin miƙa motocin ne a ranar Laraba a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa gwamnatin jihar ta samar da motocin ne a matsayin rance ƙarƙashin Tsarin Ba da Lamuni na Jihar Zamfara.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin ta ƙara samar da motocin kashe gobara guda biyar domin ƙarfafa ayyukan kashe gobara a faɗin jihar.

Da yake jawabi yayin bikin, Gwamna Dauda Lawal ya ce shirin bayar da motocin a matsayin lamuni wani ɓangare ne na manufofin gwamnatinsa na inganta tsarin sufurin jama'a, ƙarfafa tattalin arziki da kuma tabbatar da ingantaccen kuma amintaccen sufuri ga al'ummar jihar.

Ya ce, an amince motocin za su kasance ƙarƙashin kulawar NURTW, inda ƙungiyar za ta taimaka wajen tantance waɗanda za su amfana, sa ido kan yadda ake amfani da motocin da kuma tabbatar da biyan kuɗin lamunin.

Gwamnan ya bayyana cewa kowace mota ta kai darajar Naira miliyan 27.39, amma gwamnatin jihar za ta ɗauki kashi 20 cikin 100 na kuɗin a matsayin tallafi.

A cewarsa, wannan tallafin ya kai Naira miliyan 5.478 kan kowace mota, yayin da wanda ya amfana zai biya Naira miliyan 21.912 cikin watanni 44 daga ranar karɓar motar.

Gwamna Lawal ya kuma ƙaddamar da motocin kashe gobara guda biyar da gwamnatin ta saya domin inganta aikin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara.

Ya ce, gobara na iya lalata gidaje, shaguna da hanyoyin samun abinci cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, don haka sabbin motocin da aka tanada da kayan aiki na zamani za su taimaka wajen hanzarta kai ɗauki a kowane lungu da saƙo na jihar.

Ya buƙaci jami'an hukumar kashe gobara su ci gaba da horas da ma'aikatansu, wayar da kan jama'a kan hanyoyin kare kai daga gobara, tare da tabbatar da cewa motocin da kayan aikin suna cikin kyakkyawan yanayin aiki a kowane lokaci.

Gwamnan ya jaddada cewa dukkan motocin da aka raba mallakin al'ummar Jihar Zamfara ne, yana mai umartar dukkan ma'aikatu, hukumomi da masu cin gajiyar shirin da su riƙa gabatar da rahoton yadda ake amfani da kadarorin da kuma yadda ake kula da su duk bayan wata uku.

Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci lalata kadarorin gwamnati, amfani da su ba bisa ƙa'ida ba ko karkatar da su zuwa wata manufa daban ba.

No comments