Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

NAƊIN ENGR. MURTALA SHEME YA GIRGIZA ’YAN ADAWA A FASKARI

Daga Awwal Jibril Yankara Alamu sun nuna cewa naɗin Engr. Murtala Sheme a matsayin mai kula da yakin neman zaɓen ɗan takarar APC...

Daga Awwal Jibril Yankara
Alamu sun nuna cewa naɗin Engr. Murtala Sheme a matsayin mai kula da yakin neman zaɓen ɗan takarar APC, Hon. Hamza Suleman (Wanban Faskari Sadaukin Kasar Hausa na 1), ya tayar da kura tare da jefa fargaba a zukatan ’yan adawa a ƙananan hukumomin Faskari, Kankara da Sabuwa.
Tun bayan bayyana sunansa domin jagorantar harkokin yaƙin neman zaɓe na APC a yankin, jama’a da dama suka fara bayyana farin ciki da goyon baya, inda suke ganin jam’iyyar ta ɗauki mutum mai ƙwarewa, hangen nesa da kuma kusanci da talakawa.
Masu lura da al’amuran siyasa sun bayyana cewa Engr. Murtala Sheme na daga cikin matasan da suka yi fice wajen haɗa kan jama’a da tafiyar da harkokin siyasa cikin hikima da jajircewa, lamarin da ya sa wasu daga cikin ’yan adawa suka shiga tashin hankali.
Rahotanni daga yankunan Faskari da Kankara na nuna cewa wasu masu shirin yin abin da ake kira “AUNTY PARTY” sun fara sauya dabaru bayan wannan naɗi, saboda tasirin da Engr. Murtala yake da shi musamman a tsakanin matasa da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin.
Baya ga harkokin siyasa, an daɗe ana kallon Engr. Murtala Sheme a matsayin mutum mai taimakon jama’a da sauraren koke-kokensu ba tare da nuna bambanci ba. Wannan ne ya ƙara sanya mutane da dama suke ganin naɗin nasa zai ƙara wa APC ƙarfi a zaɓe mai zuwa.
Wasu daga cikin al’umma sun bayyana cewa wannan mataki ya dace ƙwarai da gaske, tare da addu’ar Allah SWT Ya ba shi hikima, nasara da kariya wajen gudanar da wannan babban nauyi da aka ɗora masa.

No comments