Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta jaridar BLUEPRINT ta 2026 kan Ingantaccen Gudanar da Dukiyar Al'u...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta jaridar BLUEPRINT ta 2026 kan Ingantaccen Gudanar da Dukiyar Al'umma da Gaskiya, saboda yadda aka yaba da salon tafiyar da albarkatun gwamnati da kuma ƙoƙarinsa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a mulkin jihar.
A cikin wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara ya sa wa hannu, ta bayyana cewa, Gwamnan ya karɓi kyautar ne ranar Talata a bikin lakca ta shekara-shekara da bayar da lambobin yabo na Kamfanin Jaridun Blueprint karo na takwas, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Taken taron na bana shi ne: “Ƙalubalen Tsaro da Amincin ZaÉ“en Nijeriya na 2027.”
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya nuna godiyarsa ga mahukuntan jaridun BLUEPRINT, tare da alƙawarin ƙara himma wajen cika manufar gwamnatinsa ta ceto da sake gina Jihar Zamfara.
Ya ce, lambar yabon ta nuna cewa kafafen yaÉ—a labarai da sauran ’yan Nijeriya da ke wajen Zamfara suna lura da irin Æ™oÆ™arin da gwamnatinsa ke yi wajen dawo da jihar kan turbar ci gaba.
Gwamnan ya ce, a cikin shekaru uku da gwamnatinsa ta yi, an samu nasarori a fannoni da suka haɗa da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki, bunƙasa jarin ɗan Adam da samar da ababen more rayuwa, yana mai cewa gaskiya da buɗaɗɗen shugabanci ne suka taimaka wajen cimma waɗannan nasarori.
A cewar jaridar BLUEPRINT, an bai wa Gwamna Lawal kyautar ne saboda tsantsar kula da albarkatun gwamnati, riƙon amana wajen harkokin kuɗaɗen gwamnati da kuma ƙoƙarin inganta tsarin mulki mai gaskiya a Zamfara.
Jaridar ta ce, kyautar ta jaddada muhimmancin gudanar da dukiyar jama’a cikin gaskiya da sanin ya kamata, tare da nuna alaÆ™ar da ke tsakanin tsauraran matakan kula da kuÉ—in gwamnati da samun ci gaba mai amfani ga kowa.
Manajan Daraktan Kamfanin Jaridun Blueprint, Salisu Umar, ya bayyana Gwamna Lawal a matsayin mutum da ya haɗa ƙwarewar aiki da hidimar al'umma.
Umar ya ce, ƙwarewar gwamnan a fannonin diflomasiyya, harkar banki da siyasa ta ba shi cikakkiyar fahimta kan shugabanci, sarrafa kuɗaɗen gwamnati da jagorancin hukumomi.
Ya ce, tun bayan hawansa kujerar gwamnan Zamfara, Lawal ya ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa hukumomin gwamnati da samar da damammaki ga bunƙasar tattalin arziki.
A cewar jaridar, gwamnatin Lawal ta mayar da hankali wajen Æ™arfafa tsarin kula da kuÉ—aÉ—en gwamnati, tabbatar da rikon amana a É“angaren gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana karkatar da dukiyar jama’a zuwa ayyukan da za su samar da sakamako mai auna tasiri ga al’ummar Zamfara.
Jaridar BLUEPRINT ta ce, Gwamna Lawal ya kasance yana jaddada muhimmancin kasafin kuɗi mai nagarta, ingantaccen samar da ayyukan gwamnati da kuma taka-tsantsan wajen sarrafa kuɗaɗen jihar a matsayin ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.
Jaridar ta kuma ce gwamnatin ta tallafa wa wasu shirye-shirye da suka shafi inganta ayyukan tsaro, kare al’ummomin karkara da samar da yanayin da zai ba mutanen da suka rasa matsugunansu damar komawa gidajensu tare da sake gudanar da harkokin rayuwa da sana’o’insu.
A ɓangaren ababen more rayuwa kuwa, jaridar ta ce gwamnatin Lawal ta ba da muhimmanci sosai wajen sake gina ababen more rayuwa a faɗin jihar.
Ta ce, gwamnati ta gudanar da ayyukan gyaran tituna da gina sababbi, inganta gine-ginen gwamnati da zuba jari a wasu muhimman ayyukan more rayuwa da aka tsara domin bunÆ™asa kasuwanci, sauÆ™aÆ™a zirga-zirga da inganta damar jama’a na samun muhimman ayyukan gwamnati.
A cewar jaridar, waÉ—annan ayyuka na da nufin sake haÉ—a al’ummomi, sauÆ™aÆ™a harkokin tattalin arziki da kuma tabbatar da ci gaba mai daidaito tsakanin birane da yankunan karkara.
Jaridar ta Æ™ara da cewa gwamnatin Lawal ta fahimci cewa ilimi na daga cikin muhimman hanyoyin rage talauci da samar da damar samun makoma mai kyau ga al’ummomi masu zuwa.
Haka kuma, ta ce gwamnatinsa ta aiwatar da wasu sauye-sauye da nufin ƙarfafa harkokin ba da kiwon lafiya a faɗin Jihar Zamfara.
Bikin ya tattaro masu tsara manufofin gwamnati, shugabannin hukumomin tsaro, ’yan siyasa, jami’an diflomasiyya, Æ™ungiyoyin farar hula, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki.
Sun gudanar da tattaunawa kan matakan da za a iya ɗauka domin tabbatar da cewa zaɓukan Nijeriya na 2027 sun kasance cikin lumana, sahihanci da gaskiya.
No comments