Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da karɓar lambar yabo da jaridar Blueprint ta ba shi ta shekarar 2025 kan ƙwarewar...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da karɓar lambar yabo da jaridar Blueprint ta ba shi ta shekarar 2025 kan ƙwarewar gudanar da dukiyar gwamnati da tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Gwamnan ya bayyana kyautar a matsayin ƙarin ƙwarin gwiwa ga gwamnatinsa wajen ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da za su inganta gaskiya, riƙon amana da kuma yadda ake tafiyar da dukiyar al’umma cikin hankali.
Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Sadarwa na gwamnatin Zamfara, Nuhu Salihu Anka, ne ya sanya hannu kan wasiƙar amincewar gwamnan, wadda ta biyo bayan sanarwar da shugabanni da kwamitin editoci na Kamfanin Jaridun Blueprint suka aika masa kan zaɓensa a matsayin wanda ya cancanta domin wannan lambar yabo.
Lawal ya nuna godiyarsa ga mahukuntan da kwamitin edita na Blueprint saboda karrama ƙoƙarin gwamnatinsa wajen inganta yadda ake amfani da dukiyar jama’a tare da ƙarfafa gaskiya da rikon amana a harkokin mulki.
Gwamnan ya ce wannan karramawa shaida ce kan aikin haɗin gwiwa, jajircewa da juriyar gwamnatinsa wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi inganta shugabanci da tabbatar da cewa ana amfani da dukiyar gwamnati yadda ya kamata.
A cewarsa, lambar yabon za ta ƙara wa gwamnatinsa ƙwarin gwiwar zurfafa manufofinta na kawo sauye-sauye masu ma’ana da tabbatar da ingantaccen shugabanci mai cike da gaskiya.
Lawal ya ce baya kallon wannan zaɓe a matsayin karramawa kawai, sai dai yana ɗaukarsa a matsayin yabo ga ƙoƙarin jami’an gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki da ke aiki domin inganta tsarin sarrafa dukiyar jama’a a jihar.
Ya ƙara da cewa karramawar za ta ƙarfafa gwamnatinsa wajen ci gaba da manufofin sauye-sauyen da ta sanya gaba, musamman matakan da aka ɗauka domin tabbatar da cewa ana amfani da dukiyar gwamnati cikin inganci, gaskiya da kuma amfanin al’ummar Zamfara.
A cikin wasiƙar, Anka ya ce gwamnatin jihar ta karɓi sanarwar zaɓen Lawal domin lambar yabo ta Blueprint ta 2025 kan Ingantaccen Gudanar da Dukiyar Jama’a da Gaskiya, tare da bayyana godiya ga mahukuntan jaridar.
Ya ce gwamnan ya karɓi zaɓen cikin farin ciki, yana kallonsa a matsayin shaida ta jajircewar gwamnatinsa da kuma ƙoƙarin da jami’anta ke yi wajen aiwatar da gyare-gyare masu ma’ana da inganta gaskiya a tafiyar da mulkin jihar.
No comments