Wata babbar tawagar Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Hon. Mani Malam Mummuni, ta kai ziya...
Wata babbar tawagar Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Hon. Mani Malam Mummuni, ta kai ziyarar taya murna ga tsohon Gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, bisa naɗa shi Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC.
Tawagar ta isar da saƙon taya murna da fatan alheri daga Gwamnan Jihar Zamfara, Mai Girma Hon. Dauda Lawal, da kuma gwamnatin jihar tare da al’ummar Zamfara, tana mai bayyana naɗin Sanata Yari a matsayin abin da ya dace da kwarewarsa da irin gudunmawar da ya bayar a harkokin siyasa da shugabanci.
A cewar Almansur Gusau, Darakta-Janar na Ofishin Yaɗa Labarai na Sanata mai wakiltar Mazabar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, Mataimakin Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa Sanata Yari zai sauke nauyin sabon muƙamin da aka ɗora masa cikin ƙwazo da himma, duba da dimbin ƙwarewarsa wajen haɗa kan jama’a a matakin ƙasa, tsara harkokin siyasa da kuma jagoranci.
Mataimakin Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da hikimar da ya nuna wajen naɗa Sanata Yari domin jagorantar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC. Ya ce naɗin ya nuna yadda Shugaban Ƙasar ya amince da ƙwarewa, cancanta da damar Sanata Yari wajen gudanar da ayyukan siyasa da haɗa kan magoya baya.
Da yake mayar da martani, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya nuna matuƙar godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal bisa ziyarar da ya kai masa a baya, tare da yaba masa kan aika wata babbar tawaga domin taya shi murnar samun sabon muƙamin.
Sanata Yari ya tabbatar wa tawagar cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa, yana mai alƙawarin amfani da ƙwarewarsa, kuzari da dabarun tsara harkoki wajen ganin an cimma manufofin da aka sanya a gabansa.
Ya kuma ce zai yi duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa ya cancanci amincewar da Shugaba Tinubu da jagorancin Jam’iyyar APC suka yi masa.
Daga cikin manyan jami’an da suka kasance cikin tawagar akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Isma’il Moriki; Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Nakwada; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamna, Alhaji Moukhtar Lugga; Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Injiniya Ahmad Yandi Gusau; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Moyi B/Magaji; da Shugaban Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, Alhaji Yahaya Abubakar Yari.
No comments