Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau (GIA) da ke Jihar Zamfara ya samu nasarar kammala dukkan gwaje-gwaje da binciken tabb...
Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau (GIA) da ke Jihar Zamfara ya samu nasarar kammala dukkan gwaje-gwaje da binciken tabbatar da inganci da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) ta gudanar, kwanaki kaɗan gabanin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci a watan gobe.
Wannan ci gaba ya zo ne yayin da ake kammala shirye-shiryen fara jigilar fasinjoji ta kasuwanci a filin jirgin, inda ake shirin samun jiragen da za su yi zirga-zirga sau biyu a mako daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa Gusau, a ranakun Litinin da Juma’a.
Wani babban jami’i a ɗaya daga cikin manyan hukumomin kula da harkokin sufurin jiragen sama na Nijeriya ya bayyana cewa, an yi wa Tsare-tsaren Gudanar da Jirgin Sama da Na’urori (Instrument Flight Procedures) na filin jirgin wani cikakken tsarin tabbatar da inganci da amincewa mai matakai 17 da ICAO ta tanada, kuma Gusau ya kammala tare da tsallake dukkan matakan.
Hukumar ICAO wata hukuma ce ta musamman ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da daidaita ƙa’idoji da dabarun zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa, tare da inganta tsare-tsare da bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da cewa suna gudana cikin aminci da tsari.
A shekarar 2023, ICAO ta gudanar da binciken tsarin zirga-zirgar jiragen sama na farar hula na Nijeriya, inda ƙasar ta samu maki kashi 75 cikin 100 na matakin aiwatar da ƙa’idojin hukumar yadda ya kamata (Effective Implementation – EI).
Sai dai a watan Afrilun 2026, ICAO ta sake gudanar da wani bincike na bibiyar matakan da Nijeriya ta ɗauka, wanda aka fi sani da ICAO Coordinated Validation Mission (ICVM), in ji jami’in.
Ya ce a lokacin, Nijeriya na fuskantar abin da ake kira “Significant Safety Concern” (SSC), wato wata babbar matsalar tsaro da ke iya zama barazana ga amincin zirga-zirgar jiragen sama.
A cewarsa, Nijeriya ta yi ƙoƙarin haɗin gwiwa wajen magance matsalar, inda aka samu nasarar warware ta cikin wa’adin kwanaki 40 da aka tsara.
Sai dai babban jami’in harkokin sufurin jiragen saman ya ce, duk da warware matsalar, har yanzu Nijeriya na da alhakin aiwatar da wasu tsare-tsaren gyara na matsakaicin zango da ICAO ta bayar da shawarar a aiwatar.
Saboda haka, an gudanar da cikakken bincike kan Tsare-tsaren Gudanar da Jiragen Sama na wasu filayen jiragen sama a Nijeriya, ta hanyar bin matakai 17 na tabbatar da inganci da amincewa da ICAO.
Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a bainar jama’a, ya ce Gusau ne kaɗai daga cikin filayen jiragen saman da aka tantance da ya samu nasarar kammala dukkan matakai 17.
“Daga cikin dukkan filayen jiragen saman da aka tantance, Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau ne kaɗai ya kammala tare da tsallake dukkan matakai 17,” in ji babban jami’in harkokin sufurin jiragen saman.
Ya ƙara da cewa shaidun da ke tabbatar da nasarar Gusau wajen kammala wannan tsari mai matuƙar buƙatar ƙwarewa na daga cikin takardun da Nijeriya ta miƙa wa ICAO.
Bayan kammala binciken ICVM, Nijeriya ta samu gagarumin ƙaruwa a matakin aiwatar da ƙa’idojin ICAO, inda makin Effective Implementation (EI) ya tashi zuwa kashi 95.1 cikin 100.
A ranar 21 ga Satumba, Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin bunƙasa hanyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Filin Jirgin Gusau da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, XEJet zai fara gudanar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci sau biyu a mako daga makon farko na watan Oktoba.
Sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen sama na Gusau da Abuja ana sa ran za ta sauƙaƙa shiga Jihar Zamfara, tare da buɗe ƙarin damammaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da masu ziyartar jihar.
No comments