Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sandunan girma da motocin aiki ga sarakunan masarautu 19 na jihar, a wani biki da ak...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sandunan girma da motocin aiki ga sarakunan masarautu 19 na jihar, a wani biki da aka gudanar a harabar Cibiyar Baje Kolin Kasuwanci da ke Gusau, babban birnin jihar.
Manyan baĆ™i da suka halarci bikin sun haÉ—a da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; Sarkin Nupe da Sarkin Gwandu.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a ranar 31 ga Oktoba, 2026.
Bayan rantsar da sarakunan, Gwamna Lawal ya miƙa sandunan girma ga sarakuna 11 masu daraja ta ɗaya da kuma takwas masu daraja ta biyu.
Haka kuma, kowanne daga cikin sarakunan da aka naÉ—a ya samu motocin aiki guda uku, waÉ—anda suka haÉ—a da motar GAC ULTRA SUV samfurin 2025/2026, motar MIKANO ZNA HILUX da kuma motar EV ANTIQUE MODEL (DDP).
Gwamnatin jihar ta ce, an samar da motocin ne domin sauĆ™aĆ™a zirga-zirgar sarakunan a faÉ—in masarautunsu, da kuma ba su damar kusantar al’ummomin da suke jagoranta.
Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan biki na nuna yadda gwamnatinsa ke girmama masarautun gargajiya a matsayin muhimman ginshiĆ™an al’umma, tare da amincewa da rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.
Ya ce bikin ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na bai wa sarakunan gargajiya martaba da goyon bayan hukumomi da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A cewarsa, sandar girma da aka miĆ™a wa sarakunan alama ce ta ikon da gwamnatin jiha ta damĆ™a musu, tare da nauyin jagorantar al’ummominsu cikin adalci, hikima, amana da tausayi.
Gwamnan ya buĆ™aci kowanne sarki da ya gudanar da aikinsa ba tare da nuna bambanci ba, ya tabbatar da adalci, tare da kula da cewa kowa a cikin al’ummarsa yana samun damar kai kukansa da neman shawarwari a fadar masarauta.
Ya ce ya kamata al’umma su riĆ™a samun shiriya, adalci da kwanciyar hankali daga wajen sarakunansu.
Gwamna Lawal ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na kammala sake gina tare da gyara sauran fadojin sarauta da ba a kammala ayyukansu ba.
Ya ce fadojin na daga cikin muhimman cibiyoyin ikon gargajiya da hulÉ—a tsakanin shugabanni da al’umma, don haka gyaransu zai Ć™arfafa masarautun tare da inganta yanayin gudanar da ayyukan sarakuna.
Dangane da motocin da aka raba, gwamnan ya ce an tanade su ne domin sauĆ™aĆ™a wa sarakunan zirga-zirga a masarautunsu, Ć™arfafa hulÉ—arsu da jama’a da kuma inganta haÉ—in gwiwarsu da hukumomin gwamnati.
Ya kuma gargaÉ—e su da su kula da motocin yadda ya kamata, tare da amfani da su bisa alhakin da aka ba su na gudanar da ayyukan sarauta.
Gwamnan ya bukaci sarakunan da su gina kyakkyawar alaƙar aiki da haɗin gwiwa tsakanin masarautunsu da gwamnatin jihar, domin cimma muradun ci gaba.
A nasa jawabin tun da farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya shawarci sarakunan da aka naÉ—a da su kasance masu cikakken biyayya ga hukumomin da suke Ć™arĆ™ashinsu. Ya kuma bukace su da su mutunta tare da kare martabar masarautun gargajiya yayin gudanar da ayyukansu.

No comments