Daga Zubairu M. Lawal Lafia Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa ta shawarci masu shirinyin zanga zanga da su zurfafa t...
Daga Zubairu M. Lawal Lafia
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa ta shawarci masu shirinyin zanga zanga da su zurfafa tunani kafin gabatar da zanga zangar.
Da yake jawabi ga manema Labarai Shugaban Jam'iyyar APC ta jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello yayi kira ga masu shirin shiga Zanga Zanga dasuyi hakuri kuma suyi tunanin makomar Najeriya.
Yace ; wannan Zanga Zangar da ake ta kokarin shiryawa ba a San suwaye jagororin wannan Zanga Zangar ba.
Yace; abune Wanda babu tsari, ba a San suwaye suka shirya ba. Kuma babu hadafi kwakwara. Yace; mutanin dake ta cewa ayi zanga zangar basu gabatar da Kansu ga jami'an tsaro cewa ga tsare-tsarensu ba.
Yace; wannan Zanga Zangar bai kamata ace mutani masu kishin kasa su shigeta ba.
Shugaban Jam'iyyar APC yace; a baya an shirya zanga zanga ta lumana a kasa, Wanda Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta.
Tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari ya taba jagorantar Zanga Zanga. Alhaji Atiku Abubakar shima ya taba jagorantar Zanga Zanga duk wadanan Zanga Zangar ansan wadanda suka shirya kuma ta lumana ne.
Amma yanzu kururuwar zanga zanga ta mamaye kasa amma an rasa sanin wadanda suka shirya jagorantar Zanga Zangar.
Ya qara da cewa masu buqatar mulki ta baya, sune ke ta kururuwar a fito Zanga Zanga domin a lalata kasa.
Burinsu a kifar da Gwamnatin da al'umman Qasa suka zabe.
Shugaban Jam'iyyar APCn yace; suma zasu fito ranar daya ga watan Augusta su zauna a sakatariyaesu su nuna goyon bayansu ga Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
Yace; idan Allah ya kaimu 2027 idan Bola Ahmad Tinubu ya nuna yana sha'awar sake tsayawa takara idan yan kasa sun bashi goyon baya za a zabeshi.
Daga karshe yayi kira ga al'umman jihar Nasarawa dasu qauracema wannan Zanga Zangar da babu tsari.
No comments