Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Daga Hussaini Yero  Gwamnatin Jihr Zamfara,karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta gabatar da taron bitar kassafin kudi ga ma...


Daga Hussaini Yero 

Gwamnatin Jihr Zamfara,karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta gabatar da taron bitar kassafin kudi ga masu ruwa da tsaki na Kananan Humumomi goma sha hudu (14)  dake fadin jihar Zamfara.

Jami'in yada labarai na m'aikatar Kananan Hukumomi, Abdullahi Muhammad Birnin Magaji ne ya bayyana haka a takardar da yasa mahañnu ga manema labarai a Gusau. 

Acewar sa, Ma'aikatar Kananan Hukumomi karkashin jagorancin Kwamishina, Hon Ahmad Garba Yandi ne ta jagoranci ,gudanar da bita na tsawon Kwanaki uku ga masu ruwa da tsaki,na Kananan Hukumomin a bangaren kasafin kudi.wadanda suka hada da Shugaban Karamar Hukuma da Ma'aji da Daraktan Tsare tsare.

A taron masana sun gabatar da jawabai akan yadda ake gudanar da tsarin Kasafin kudin,a aikace da kuma yadda ake gyara idan an samu gibi .

Kwamishinan Kananan Hukumomi Hon Ahmad Garba Yandi a jawabin sa, ya bayyana cewa,sun shirya wannan bita ne domin gano kurakuren da aka samu a Kasafin kudin shekara da ta gabata,ta yadda a Kasafin kudin na 2024 ya kasance,babu matsala acikin .

Akan haka ne, Hon Yandi yayi kira ga masu bitar da su kasance sun amfana da wannan bita dan samun nasara a Kasafin kudin na shekara Mai zuwa.

Anasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kananan Hukumomi a Majalisar Dokoki ta Jihr Zamfara,Hon Hamisu A.Faru ya bayyana cewa,wannan bitar anyita daidai lokacin da ya dace,kuma da yardar Allah da zarar kasafin kudin ya iso zauran majalisa zamuyi iya kokarin wajan ganin anduba shi bisa lokaci dan cigaba da ayyuka ga alumma Jihr Zamfara.

Odita Janar na Kananan Hukumomi,Aminu Mamanga ya tabbatar da cewa, Ma'aikatan sa zasubi didigi Kwabo da Kwabo wajan gudanar da Kasafin be kudi.

A karshe , Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) Hon Kasimu Kaura ya tabbatar da cewa,wannan bitar kwaliya zata biya kudin sabulu kuma zata taimaka mana wajan ganin Kasafin kudin na shekara mai zuwa ba asamu tsaiko ba ballantana matsala.da yardar Allah.

No comments