Daga Abubakar Rabilu , Gombe Masana a jihar Gombe, a ranar Laraba sun bayyana cewa shirin Adolescent Girls Initiative for Learn...
Daga Abubakar Rabilu , Gombe
Masana a jihar Gombe, a ranar Laraba sun bayyana cewa shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) wanda Bankin Duniya ke tallafawa zai inganta damar ‘yan mata na samun ilimi a jihar.
Sun bayyana hakan ne a yayin taron yini daya na tattaunawa da wayar da kai ga kungiyoyin agaji, CBOs da kungiyoyin farar hula (CSOs) da aka gudanar a Gombe.
Dakta Amina Abdul, shugabar shirin AGILE a jihar Gombe, ta ce shirin zai mayar da hankali ne kan karfafa ‘yan mata ta hanyar ilimi.
Abdul ta ce burin shirin shi ne inganta damar samun ilimin sakandare tsakanin ‘yan mata masu shekaru 10 zuwa 20 ta hanyar magance matsalolin da ke hana su samun ilimi.
A cewarta, ‘yan mata da suka daina makaranta za su sami damar cigaba da karatunsu a cikin jihar ta hanyar shirin AGILE.
Ta bayyana cewa shirin wanda za a kaddamar nan bada jimawa ba, zai mayar da hankali wajen yi wa ‘yan mata 10,000 rijista a fadin jihar.
“Shirin ba zai yi tasiri ba idan ba a sami karin adadin ‘yan mata da ke shiga makaranta ba. “Yanzu haka, ‘yan mata da yawa suna barin makaranta kuma manufar shirin shi ne dawo da ‘yan matan makaranta domin mu sami ingantacciyar al’umma.
“Manufarmu ita ce samun ‘yan mata dubu 10,000 su koma makaranta kuma muna fatan samun wannan adadi domin kuwa ba wai ba su nan ba ne, sai dai iyayensu ba su shirya tura su makaranta ba. “Muna da niyyar isar da wannan sakon ga iyaye da al’umma domin dawo da su makaranta,” in ji ta.
Abdul ta ce domin cimma manufar shirin a jihar, za a aiwatar da tsare-tsare da dama kamar bayar da tallafin karatu ga ‘yan mata, gyaran makarantu da kuma shigar da iyaye cikin shirin.
Misis Gloria Usman, Daraktar kungiyar Voice of Hope, wata kungiya mai zaman kanta ta yaba wa shirin AGILE wanda ta ce zai taimaka wajen magance matsalolin da ke hana ‘yan mata samun ilimi.
Usman ta ce tun da ‘yan mata sune mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar, ya kamata a samar da karin shirye-shirye kamar AGILE domin karfafa ‘yan mata ta hanyar ilimi.
Sai dai, ta yi kira da a tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata daidai da manufarsa, domin ‘yan mata su sami damarmaki na gari ta hanyar ilimi don cimma burinsu a rayuwa.
Dokta Ishiyaku Adamu, shugaban kungiyar JONAPWD na jihar ya ce shirin dama ce da za ta taimaka wajen magance kalubalen da ke hana yaran samun ilimi a jihar.
Adamu ya yi kira da a bai wa yara masu bukatun musamman fifiko ta hanyar yi musu rijista, samar da kayan aiki da kuma horas da malamansu. “Muna son makarantu masu daukar kowa da kowa a waje daya; yara masu bukatu na musamman da wadanda ba su da bukatu na musamman suna karatu a wuri daya.
“Wannan zai taimaka wajen kawar da bambanci domin ware su (yara masu bukatu na musamman) ba abin karfafa gwiwa bane,” in ji shi.
No comments