Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Mai kwarya ya zama sabon Madakin Kwandare

Daga Zubairu M. Lawal Lafia  Masarautan Kwandare dake karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa ta nada Alhaji Muhammadu Abubakar M...


Daga Zubairu M. Lawal Lafia 

Masarautan Kwandare dake karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa ta nada Alhaji Muhammadu Abubakar Maikwarya a matsayin sabon Madakin Kwandare.

Taron da ya gudana a garin Kwandare ya samu hakartan manyan baki da masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya.

Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya Madakin Kwandare shine Shugaban kungiyar durebobin sufuri ( NURTW) ta jihar Nasarawa.

Kafin nadinsa a matsayin Madakin tunda farko shine Bunun Kwandare.

Da yake jawabi a wajen taron Mai martaba  Sarkin Lafia  Mai Shari'a Sidi Bage Muhammad. Wanda ya samu wakilcin madakin lafiya Alhaji Dauda Isyaka.  yayi fatan alheri ga wadanda aka nadasu wadanan sarautun.

Yace wadanda aka basu sarautan sun cancanta, zasu kawo cigaba a wannan masarautan.

Sannan masu sarautan su kasance tare da sarki lokaci bayan lokaci. Masamman ranar juma'a ayi sallah tare da sarkin.

Shima uban taro Sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Al-makura, yayi godiya ga alumman da suka taru. Yayi godiya da samun Asibiti koyarwa na Jami'ar Gwamnatin tarayya a grain Lafia.

Ya yabawa jigajigan dake tafiyar da masarautan lafia da suke tafiyar da harkokin lafiya koda babu sarki a kasa.

Yayi godiya ga sarakunan da sauka halarci bikin, da yan siyasa.

Shima Uban gyayya Sabon Madakin Kwandare Shugaban Kungiyar Direbobin sufuri Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya, ya bayyana farin cikinsa da dubban al'umman da suka zo na nesa da na kusa.

Madakin Kwandare ya jinjinawa Sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Al-makura tare da masu ruwa da tsaki a masarautan da sukaga cancantarsa da rike wannan sarautan.

Madakin yayi alkawarin kawo cigaba  da kara tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al'umman Kwandare baki daya.

Madakin yace; babu abinda zai cema al'umman da suka taru sai dai yayi fatan Allah ya koma da kowa gidan sa lafiya.

Garkuwan Kwandare Alhaji Faisal Ahmad Al-makura yayi firin ciki da godiya ga masarautan Kwandare da ta duba cancantarsa ta nadashi a matsayin Garkuwa. Yace; zaiyi amfani da damarsa na matashi ya hada kan matasan Kwandare wajen samun cigaba.

Masarautan Kwandare ta nada mukaman dabam dabam

No comments