Daga Ibrahim Muhammad Kano. Alhaji Abubakar Lawan Jinjiri shugaban jam'iyyar NNPP na karamar hukumar Kiru ya bayyana cewa da...
Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Alhaji Abubakar Lawan Jinjiri shugaban jam'iyyar NNPP na karamar hukumar Kiru ya bayyana cewa daruruwan magoya bayan yan jam'iyyar APC ne suka dawo jam'iyyar su ta NNPP saboda gamsuwa da akidar kawo cigaba ta jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da yan jarida a lokacin da ya jagoranci wadanda suka sauya sheka yin mubaya'a ga jagoran Kwankwasiyya dakta Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa dake kan titin mila.
Ya ce shi yasan yaro da jagoransu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu kasar waje alhali iyayensa basu da kudinda za su biya wa kansu suje ko da Abuja, amma sai ga dan su yaje Indiya yayi karatu ya zama injiniya yanzu yana aiki yana taimakon iyayensa da makota da al'ummar su
Ya kara da cewa ganin irin raya cigaban al'umma da raya kasa da kyakkyawan nufi da na zuciya da Kwankwaso yake da ita ake gani a aikace a fannoni daban daban shi yasa mutane keta tururuwar shigowa cikin tsarin tafiyar Kwankwasiyya .
Ya ce ga wadanda suka shigo jam'iyyar NNPP a yanzu tsarin Kwankwasiyya duk an zama abu daya da wadanda suka samu a ciki kuma tun daga mazaba har karamar hukuma za a yi musu adalci kamar yanda jagora ya tabbatar masu.
Alhaji Abubakar Jinjiri ya ce duk jiga-jigan yan hamayya a kiru suna waje daya suka zo da. NNPP suka ci sanata da dan majalissar jiha dana tarayya a yankin kiru Abba Kabir Yusuf ya ci Gwamna Kwankwaso ma ya ci zaben shugaban kasa basu taba faduwa ko akwati daya yan hamayya basa ci dama mun fi karfinsu basu sun mutu mushen gizaka ne.
Shima jagoran Kwankwasiyya na karamar hukumar Kiru .Hon.Bello Aliyu Kiru yace mutum 1,673 ne suka dawo jam'iyyar NNPP daga mazavun 15 karkashin Dattijai guda biyu da matashi guda daya.Alhaji Lawan Dalha shugaban Dattawa na APC na kiru da tsohon dan majalisa a jamhuriya ta biyu Alhaji Aminu Lawan lwanar Dangora Dattijo ne mai kyakkywan mu'amala da ya san jiya da yau.
Ya kara da cewa akwai kuma shugaban matasa da a baya suka bi wani mutum mai son biyan buƙatar kansa sai daga baya suka farga suka dawo karkashin Mahmud a Tela Kwanar Dangora sune jagorori da suka jawo wadannan dinbin tsofaffin yan APC suka dawo cikin gidan Kwankwasiyya me daraja.
Hon.Bello Aliyu Kiru ya ce akwai ma tsohon sakataren ilimi na Kiru Balarabe Zubairu mai hoto da tsohon sakataren mulki na karamar hukumar Kiru yanzu sun dawo gidan injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Wadanda suka
No comments