Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya barranta kansa da hannun a wata kungiyar ...
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya barranta kansa da hannun a wata kungiyar magoya baya dake ikirarin kiran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bijirewa Kwankwaso mai suna ”ABBA TSAYA DA ƘAFARKA”.
Baffa Bichi ya ce babu wata kungiya da yake da hannu ciki makamanciyar hakan dan haka ba shi da wata alaka da ita.
Sakataren gwamnatin ya ce in ban da Kungiyar (One to Tell Tell) da yake da ya yi yakin neman zaben shugaban kasa a fadin jihohin Arewa 19 da ake da su bai san wata kungiya ba.
Ya ce; "Muna yi wa Gwamna biyayya
da Jagoranmu na darikar Kwankwasiyya na duniya Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso bisa haka ni ba ni da wata masaniyya kan wancan batun wata kungiya da ake alakanta ta da ni."
No comments