Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal zai karbi baƙuncin ɗaukacin gwamnonin jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki, inda za su tattau...
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal zai karbi baƙuncin ɗaukacin gwamnonin jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki, inda za su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam'iyyar da ƙasa baki ɗaya a Gusau, babban birnin jihar.
Yau Juma'a ne ake sa ran isar gwamnonin a Gusau don shirin taron da zai gudana a gobe Asabar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa gwamnonin PDP É—in za su tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da dabarbarrun ta, musamman a yanayin juyawar siyasar da ake ciki.
Sanarwar ta Idris ta kuma bayyana cewa, Gwamna Dauda Lawal ya na matuƙar maraba da gwamnonin na PDP zuwa jihar Zamfara. "Gwamnonin za su iso ne yau don halartar wani muhimmin taron ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP."
"Gwamna Lawal zai ci abincin dare yau tare da gwamnonin, kafin zaman nasu da za su yi na sirri a gobe.
"Wannan taro zai samar wa shugabannin jam'iyyar daman tattauna muhimman batutuwan jam'iyyar, tare da tsara hanyar samun haÉ—in kan jam'iyyar, da kuma tattauna batutuwan da za su ciyar da jihohin nasu gaba.
"Bugu ta ƙari, gwamnonin za su tattauna muhimman batutuwa game da shirye-shiryen babban taron jam'iyyar na ƙasa wanda zai gudana a Ibadan ta jihar Oyo a ranakun 15 da 16 na watan Nuwambar 2025," in ji sanarwar ta Kakakin Gwamnan.
No comments