Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Auyo, Kafin Hausa da Hadejia a jihar Jigawa, Hon. ...
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Auyo, Kafin Hausa da Hadejia a jihar Jigawa, Hon. Usman Ibrahim Auyo, wanda aka fi sani da Kamfani, ya jajanta wa al'ummar garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa bisa barna da fashewar tankar man fetur, wanda ya jawo salwantar rayuka sama da 100, tare da jikkata mutane masu yawa.
Hon.Usanan Ibrahim Auyo ya ce yana nuna damuwarsa da bakin ciki da alhini, sannan sai ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunar musiba.
Ya yi addu'ar Allah ya ya bai wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu dangana da hakuri. Ya ce, "Wannan rashin nasu gaba daya. Muna addu'ar wadanda suka jikkata Allah ya ba su lafiya cikin gaggawa."
Hon. Auyo ya mika sakon ta'aziyya da jaje a kan wannan rashi ga al'ummar Majiya da gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Malam Namadi Danmodi da fatan Allah ya kare aukuwar hakan a nan gaba.
No comments