Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ta'amali da miyagun kwayoyi na dashe basirar matasanmu

Inji Gwamna Sule  Daga Zubairu Lawal  Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yace ta'amali da miyagun kwayoyi daya zama ruw...

Inji Gwamna Sule 

Daga Zubairu Lawal 

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yace ta'amali da miyagun kwayoyi daya zama ruwan dare a tsakanin matasanmu yakan janyo dishewar basirar da suke dashi.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakane ranar laraba a taron wayar da kai na yini biyu kan yaki da ta'amali da miyagun kwayoyi.

Gwamanan yace wannan babban kalubalene masamman ga al'umman Arewaci saboda ta'amali da miyagun kwayoyi ya zama abin birgewa wajen matasa da matan aure abin bakin ciki har da yara kanana.


Yace; yanzu shaye-shaye ya zama abin gadara ga dalubai dake manyan makarantu da kanana, tayaya matasa zasu samu basirar kera wani abinda zai amfanesu da kasarsu.

Gwamnan yayi kira ga iyaye da malamai da kunhiyoyi da hukuma cewa ya zama wajibi mutashi tsaye domin kawar da wannan dabi'ar.

Shima a nasa jawabin Shugaban kwamitin yaki da miyagun kwayoyi a majalisan wakilai ta kasa Hon. Abbass Adigun Agboworin,  ya yabama wannan taron. 

Yace; ya zama wajibi ga kowa da kowa ya kawo gudumawarsa domin kawar da miyagun kwayoyi a Nijariya.

Yace ta'amali da miyagun kwayoyi ya shiga gida gida da makarantu da sauransu.

Yace; wadanda muke gadara da su sune matasa kuma sune suka fada cikin wannan rayuwar ta shaye-shaye.

Shima a nasa jawabin  kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Hon. Gaza Gwamna yace ta'amali da miyagun kwayoyi ya kawo koma baya so sai wajen samu ilumi mai inganci ga matasanmu.

Yace; yanzu mafi yawan masu kamuwa da cutar hauka matasane. Kuma ta sanadiyar ta'amali da miyagun kwayoyi ne.

Yace ta'amali da miyagun kwayoyi yana janyo durkushewar tattalin arziki a kasa.

Itama a nata jawabin Hajara Ibrahim Dan yaro yar Majalisan dake wakiltar Nasarawa ta tsakiya a majalisan dokoki ta jihar Nasarawa. Tace ya zama wajibi Gwamnati da Malamai da iyaye su mike tsaye wajen kawo karshen ta'amali da miyagun kwayoyi a Nijariya.

Tayi kira ga mata dasu daina ta'amali da miyagun kwayoyi saboda suke bada tarbiya. bai kamata uwar dake renon yara su zama nagari a sameta da shaye-shaye ba. Ya zama kenan yaran zasu iya yin koyi da rayuwar ta.

Dole sai ka gyara kanka kake zama nagari mutumin kirki.

Abin bakin ciki uwa ta zama mai harkan shaye-shaye. To wani irin tarbiyane yaranta zasu samu daga gareta? 

Dan yaro tace yara su na samun cikaken tarbiya daga uwance to idan uwa ta lalace wani tarbiya yaro zai samu

No comments