Daga Zubairu Lawal Da yake jawabi ga manema labarai Dr. Paul Agbo wanda likitani a bangaren masu fama da cutar matsakar kwakwal...
Daga Zubairu Lawal
Da yake jawabi ga manema labarai Dr. Paul Agbo wanda likitani a bangaren masu fama da cutar matsakar kwakwalwa a Asibitin koyarwa ta jami'ar Gwamnatin tarayya dake garin lafia.
Yace; yawan zurfafa dogon tunani yakan janyo matsalar kwakwalwa.
Dr. Paul ya bukaci al'umma su rage dogon buri da ke sanyasu shiga tunani na rashin tabbas.
Yayi kira ga jama'a dasu rika zuwa gurin kwararun likitochi a Asibiti ana duba lafiyan kwakwalwarsu domin kwaucewa matsala.
Yace; lalurar matsalar kwakwalwa abune da yanzu yake addabam dubban mutani maza da mata manyan dayara a Nijariya.
Saboda haka akwai bukatar kare kai daga kaucrwa barazanar kamuwa da cutar.
Dr Paul Agbo yayi kira ga al'umma dasu kaucewa zaman kadaita dake sanya mutum ya shiga tunani mara dalili. Yayi kira ga al'umma dasu rika zama a guraren walwala da nishadi.
Haka zalika ya bukaci iyaye maza da mata dasu sanya ido kan yara domin kaucewa ta'amali da miyagun kwayoyi dake jefa rayuwar matasa cikin halin kuncin rayuwa.
Daga karshe yayi kira ga al'umma dasu rika mutsa jiki da yawan kallace-kallace dake sanya nishadi.
Sannan an bukaci kungiyoyi dasu zama masu wayar da kan al'umma.
No comments