Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa yadda suka kama wasu makamai da ake jigilar...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa yadda suka kama wasu makamai da ake jigilarsu zuwa jihar.
A ranar Talatar da ta gabata ne Daraktan Hukumar a jihar ta Zamfara ya baje kolin makamai da alburusai da aka kama ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, makaman da aka kama sun haɗa da bindigar RPG, manyan bindigogin 'Machine gun' guda biyu, bindigogi ƙirar AK47 guda tara, bindigogi ƙirar pistol guda biyu, mujallar alburusai guda goma sha tara, da sama da ɗaiɗaikun alburusai guda dubu.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin É—an bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.
Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haÉ—in gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaÆ™i da ‘yan bindiga.
“Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.
“Ina so in jaddada cewa waÉ—annan nasarori da aka samu tare da wasu na daÆ™ile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haÉ—in kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa É—aukacin jami’an tsaro.
“Za mu ci gaba da tallafa wa sojojin ta kowace hanya da za mu iya don Æ™arfafa musu gwiwa su ci gaba da gudanar da ayyukansu.
“Zan yi farin ciki sanin cewa yawancin wafannan miyagun ‘yan asalin Zamfara ne. Ba baÆ™i ba ne, kuma wannan mutumin da aka kama ba shi kaÉ—ai ba ne. Mun sami ire-iren waÉ—annan a cikin ’yan makonnin da suka gabata, amma wannan shi ne kaÉ—ai muke gabatarwa ga jama'a. Irin wannan kamun na faruwa a kullum.
“’Yan bindiga na raguwa a Zamfara. Mun ga haka. Na buÆ™aci al’ummar Zamfara da su bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suka dace.
No comments