Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

KWAMISHINAN MUHALLI NA JIHAR KATSINA YA RABA KUDI DA KAYAN ABINCI

Daga Awwal Jibril 'Yankara A ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, 2025, Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sulaiman ...


Daga Awwal Jibril 'Yankara

A ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, 2025, Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sulaiman Faskari, wanda aka fi sani da Wanban Faskari kuma Sadaukin Kasar Hausa, ya raba tallafin kudi sama da Naira miliyan hamsin (#50,000,000) tare da buhunnan gero, shinkafa da masara guda 500 kowanne.

Taron rabon tallafin ya gudana a harabar Sakatariyar Karamar Hukumar Faskari, inda dubban jama'a suka halarta, ciki har da magoya bayan jam’iyyar APC daga kananan hukumomin Faskari, Funtua, Kankara, Sabuwa da Musawa.

Alhaji Bala Musawa, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, shi ne babban bako mai jawabi a wajen taron. A cikin jawabinsa, ya bayyana cewa wannan shine karo na 12 da Hon. Hamza Sulaiman Faskari ke gudanar da irin wannan gagarumin tallafi. Ya ce farkon wannan taimako ya fara ne da Naira dubu dari shida (#600,000), amma a duk shekara adadin tallafin na karuwa, har ya kai ga sama da Naira miliyan hamsin a wannan karo.

Shugaban Yada Labarai na jam'iyyar APC na jihar Katsina ma ya yaba da kokarin kwamishinan bisa irin gudunmawar da yake bayarwa don tallafa wa al’umma.

A nasa jawabin, Hon. Hamza Sulaiman Faskari ya gode wa Allah da ya ba shi ikon taimaka wa jama'a. Ya bayyana cewa taimako ba wai iyawa ba ne, sai dai ikon Allah da ya ba mutum damar taimakawa. Haka nan, ya yi addu’a Allah ya tona asirin duk wanda ke da hannu a matsalar tsaro, ko dan siyasa ne, ko malami, jami’in tsaro, jami’in gwamnati, mai kudi ko talaka.

No comments