Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa adadin haɗurran mota a jihar Zamfara ya ragu da kashi 6 cikin 100 idan aka...
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa adadin haɗurran mota a jihar Zamfara ya ragu da kashi 6 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, sakamakon aiwatar da sabbin manufofin tsare-tsare da sabunta birane a jihar.
Kwamandan sashen FRSC na Zamfara, Aliyu Ma’aji, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Gusau domin ƙaddamar da shirin wayar da kai na “Ember Months” na shekarar 2025. Ya ce a bana, hukumar ta yi rijistar haɗurra 46, idan aka kwatanta da 56 a bara, wanda ya yi daidai da ragin kashi 6.27.
Ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata, mutane 51 ne suka rasa rayukansu, yayin da 259 suka ji rauni sakamakon haɗurra. Ya danganta yawan mace-macen ga haɗa kaya, dabbobi da mutane cikin manyan motoci na ɗaukar kaya — dabi’a da ya ce ta jima tana haddasa mummunan sakamako.
A cewar Ma’aji, taken kamfen na bana, “Ka ɗauki Nauyin Tsaron Kanka: Guji Tuƙi Cikin Hargitsi,” na nuni da cewa kuskuren ɗan Adam shi ne babban abin da ke kawo haɗurra a hanya. Ya ce gajiyar direbobi, cunkushe fasinjoji, jigilar mutane cikin manyan motoci masu ɗaukar kaya da safarar man fetur a cikin kwantena na roba, sune manyan dalilan hatsarori.
Ya kuma nuna cewa hukumar ta tanadi tsare-tsare na musamman domin tabbatar da nasarar shirin karshen shekara.
A matakin ƙasa, Rahoton hukumar ya nuna cewa mutane sama da 3,400 sun rasu a cikin haɗurra a faɗin Najeriya daga Janairu zuwa Satumba 2025, saboda sakacin direbobi da muguwar amfani da hanya. Babban kwamandan FRSC, Shehu Mohammed, ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da kamfen ɗin wayar da kai na Ember Months.
A cewarsa, cikin watanni tara, an samu haɗurra 6,858 inda mutane 3,433 suka rasa rayukansu, yayin da 22,162 suka ji rauni. Ya bayyana cewa mafi yawan waɗannan haɗurra na iya kaucewa, da ace an bi ƙa’idojin tuki da kiyaye hanyoyi yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa kamfen ɗin zai ci gaba daga 15 ga Disamba zuwa 15 ga Janairu, domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan ƙarshen shekara, lokacin da haɗurra kan ƙaru.
No comments