Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Tsofaffin Manyan Sakatarori Sun Karrama Gwamna Lawal, Sun Yaba Da Ayyukan Ci Gaban Zamfara

Ƙungiyar Tsofaffin Manyan Sakatarori na Jihar Zamfara ta karrama Gwamna Dauda Lawal tare da yaba wa ayyukan ci gaban da gwamnati...

Ƙungiyar Tsofaffin Manyan Sakatarori na Jihar Zamfara ta karrama Gwamna Dauda Lawal tare da yaba wa ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa a faɗin jihar.

An miÆ™a masa lambar yabo ta girmamawa ne a ranar Juma’a a É—akin taro na Gidan Gwamnati da ke Gusau, yayin wani taro da ya haÉ—a manyan tsofaffin jami’an gwamnati da suka yi wa jihar hidima tsawon shekaru.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Æ™ungiyar ta bayyana manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin Lawal ta aiwatar a matsayin dalilin ba shi wannan karramawa. 
Sun nuna cewa sauye-sauyen da aka samu a fannoni da dama sun sa suka ga ya dace su girmama gwamnan bisa ƙoƙarinsa.

Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon, Gwamna Lawal ya gode wa ƙungiyar bisa ganin ya cancanci wannan girmamawa, yana mai cewa babu wata karramawa da ta wuce wadda ta fito daga hannun manyan mutane da suka shafe rayuwarsu suna hidimta wa jiha cikin gaskiya da ƙwarewa.
Ya ce, duk da an shirya masa liyafar girmamawa, rashin lokaci ya hana hakan tabbata, amma hakan ba zai rage darajar wannan karramawa a gare shi ba. Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki ne bisa gaskiya da riƙon amana, kuma tun kafin hawansa mulki ya tsara manufofi shida da suka zamo tubalin jagorancin gwamnatinsa.

A cewarsa, tsaro shi ne ginshiƙin farko a cikin manufofin, kuma ana samun gagarumin ci gaba a bangaren. Ya kuma bayyana cewa ana aiwatar da ayyuka a dukkan ƙananan hukumomin jihar domin buɗe ƙofar zuba jari da habaka tattalin arziki.

Ya Æ™ara da cewa, ana sa ran kammala aikin filin jirgin saman Æ™asa da Æ™asa na jihar cikin ‘yan watanni masu zuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa babu Æ™aramar hukuma a Zamfara da ba a zuba sama da naira biliyan ashirin a ayyukan ci gaba ba, yana mai kira ga jama’a su duba ayyukan da ke gudana domin ganin sauyin da ake samu da idanunsu. 

Haka kuma ya ce ana samun sauƙin matsalolin tsaro a hankali, yayin da kuɗaɗen shiga na cikin gida suka tashi daga kimanin Naira miliyan tamanin zuwa sama da Naira biliyan biyar.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Muhammad Bello Umar, ya ce sun yanke shawarar karrama gwamnan ne saboda irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan fara aikinta a 2023.

Ya ce tun daga farko gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwa da jajircewa ta hanyar fito da ajanda shida, wadda a cewarsa ta zarce tsammanin da dama.

Ya kuma tuna cewa a wani taronsu na baya, sun roƙi a biya bashin hakƙoƙin ritaya, kuma gwamnati ta amsa buƙatar tare da biyan sama da Naira biliyan goma sha uku da ake bin gwamnati.

A cewarsa, tarihin Zamfara ba zai manta da Gwamna Lawal ba saboda irin tasirin ayyukansa ga ma’aikata, lafiya, ilimi da sauran manyan ayyukan more rayuwa.

No comments